Ashariyar da wasu aku 5 ke yi wa mutane a gidan zoo yasa dole an raba su (Hotuna)

Ashariyar da wasu aku 5 ke yi wa mutane a gidan zoo yasa dole an raba su (Hotuna)

- An raba wasu aku 5 da suka addabi mutane da ashariya a gidan kula da namun daji da ke Birtaniya idan suna tare

- Shugaban gidan namun dajin ya ce mafi yawancin tsintsayen ba su cika magana ba idan sun ga mutane amma wadannan sun fita daban

- Ya ce an raba su ne saboda kada yara da ke zuwa kalon namun daji a gidan su koyi ashariya daga bakinsu

Wani gidan zoo na kula da namun daji da ke Birtaniya ya raba wasu aku guda biyar saboda yawan dirka wa masu kai ziyara gidan ashariya da su keyi kasancewarsu a wuri daya.

An kawo akun biyar gidan kula da namun daji na Lincolnhire Wildlife Centre ne a watan Agustan shekarar 2020 amma a halin yanzu an boye su cikin wannan makon kamar yadda The Associated Press ta ruwaito.

An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna)
An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna). Hoto: @Lindaikeji
Asali: Twitter

"Ba sune aku na farko da mukayi da su ke yin ashariya ba, amma bamu taba samun guda biyar a lokaci guda ba," a cewar shugaban gidan zoo din, Steve Nichols.

"Galibin akun da muke da su ba su magana idan an fito da su waje amma wadannan biyar din sun fita daban saboda ashariyar."

KU KARANTA: Na kashe fiye da mutum 50 don sun kasa biyan kudin fansa - Shugaban masu garkuwa

An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna)
An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna). Hoto: @Lindaikeji
Asali: Twitter

A cewar Nichols, babu wanda ya yi korafi a kan ashariyar da akun ke yi cikin masu kawo ziyara gidan, mafi yawancin su ma sha'awa abin ke basu.

"A lokacin da aku ya dirka ashariya, ya kan burge mutane sosai," kamar yadda ta ce a ranar Talata. "Hakan ya saka mutane da dama sunyi raha a wannan shekarar mai wahala."

Nichols ya ce an raba akun ne domin gudun kada yara su koyi ashariyar daga bakinsu.

An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna)
An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna). Hoto: @Lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: 'Yan sanda sun yi holen 'yan fashi da makami da masu garkuwa a Abuja

An raba su an kai su wurare daban-daban a gidan ta yadda ba za su rika "ingiza juna ba," inji shi.

Nichols ya shaida wa BBC cewa akun su kan yi ashariyar ne domin mutane su tanka musu,"don haka ganin yadda abin ke bawa mutane mamaki ko burgesu yakan sa su cigaba da ashariyar."

An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna)
An raba wasu aku 5 a gidan zoo saboda yi wa mutane ashariya (Hotuna). Hoto: @Lindaikeji
Asali: Twitter

"Idan dukkansu biyar suna tare, daya zai yi ashariya sai daya ya kama dariya sai wani ya dauka," in ji shi.

"Ina fatan za su koyi wasu kalaman a zoo din," Nichols ya kara da cewa. "Amma idan suka cigaba da koya wa sauran zagi zamu samu tsuntsaye 250 masu yin ashariya, Ban san abinda za muyi ba," in ji shi.

A wani rahoton,Yan sanda a Enugu sun kama wani mutum da ya shiga wani wurin bauta ya kama abin bautar da ya ce ya hana mutanen garin cigaba, ya yi sanadin tabarbarewar kasuwanci tare da hana 'yan mata samun mazan aure.

Mutumin mai matsakaicin shekaru, Nnajiofor Donatus ya ce wahayi aka masa ya tafi ya cire abin bautar daga inda ya ke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel