Takardar dokar sayar da NNPC ta wuce matakin farko a majalisar dattawa

Takardar dokar sayar da NNPC ta wuce matakin farko a majalisar dattawa

- Farawa da iyawa, yan majalisa sun shiga aikin kan dokar sayar da NNPC

- Yan majalisan sun koma bakin aiki bayan makonni na hutu

Takardar dokar sauye-sauye a masana’antar feturin Najeriya PIB 2020 ta tsallake mataki na farko a majalisar dattawa ranar Laraba.

Yayin zama a zauren majalisa, Shugaban majalisar, Ahmed Lawan, ya bada umurnin a baiwa dukkan Sanatoci takardar ranar Alhamis.

A jiya mun ruwaito muku cewa Karamin ministan man fetur, Temipre Sylva, ya yi fashin bakin kan lamarin dake tattare da dokar sauye-sauye a cikin kamfanin man feturin kasa watau NNPC da ya aikewa majalisar dokokin tarayya.

Ministan ya bayana cewa ba shafe kamfanin NNPC za’ayi ba, face sayar da ita kawai.

Ya bayyana hakan ne yayında yaka hira da manema labarai ranar Litinin bayan ganawarsa da shugabannin majalisar dokokin tarayya.

KU KARANTA: Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

Takardar dokar sayar da NNPC ta wuce matakin farko a majalisar dattawa
Takardar dokar sayar da NNPC ta wuce matakin farko a majalisar dattawa
Source: Facebook
Mun ji maganganu iri-iri kan cewa za’a shafe NNPC amma babu abu mai kama da hakan cikin abinda muka gabatar. Ba za’a staffe NNPC ba amma za’a sayar da ita bisa ga sharrudan sauye-sauyen da aka aiwatar kan dukkan rasen man fetur a kasar nan, “ Yace

DUBA NAN: Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

Bayan tattaunawarsu, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya yi alkawarim kafa tarihi ta hanyar tabbatar da cewa dokar ta samu gindin zama wannan karon.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ga majalisar dokokin tarayya makon gobe, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya laburta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel