'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya roki gwamnatin tarayya ta gayyaci sojojin Chadi su taya ta yaki da Boko Haram

- Gwamna Zulum ya yi wannan kirar ne yayin da tawagar kungiyar gwamnonin Najeriya ta ziyarce shi a Maiduguri babban birnin jihar Borno

- Zulum ya ce babu wata soja a duniya da ta ci galaba a kan 'yan ta'adda ba tare da hadin gwiwa da wasu sojojin ba

Babagana Zulum, gwamnan jiha Borno ya roki gwamnatin tarayyar Najeriya ta nemi taimakon sojojin kasar Chadi wurin yaki da 'yan ta'adda kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A cewar Abdulrazaque-Barkindo, kakakin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Zulum yi wannan jawabin ne yayin da ya tarbi wasu gwamnoni a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Laraba.

'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari
'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Wasu da ake zargi 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram ne sun kai wa tawagar gwamnan hari sau biyu cikin kwanaki biyar da suka shude.

DUBA WANNAN: An sace shugaban karamar hukuma a hanyarsa ta zuwa gona a Kaduna

Gwamnan ya ce hare-haren ba zai hana shi cimma abinda ya saka a gaba ba.

"Zulum ya roki gwamnatin tarayya ta tabbata ta gayyaci sojojin Chadi su taimaka wa sojojin Najeriya wurin yaki da 'yan ta'addan idan har ana son samun nasara," a cewar sanarwa.

"Zulum ya ce babu wata rundunar soji a duniya ta yi nasarar kawar da ta'addanci ita kadai hakan yasa ya bukaci gwamnatin tarayya ta duba hanyoyin da za ta yi aiki da sojojin Chadin don taimakawa sojojin Najeriya don kawo karshen ta'addancin cikin kankanin lokaci."

Ya koka ka yadda 'yan ta'addan suka mamaye dajin Sambisa da Tafkin Chadi suka kori miliyoyin al'ummar da ke zaune a yankunan a baya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

Kayode Fayemi, shugaban kungiyar gwamnoni, NGF, wadda ya jagoranci tawagar ya ce duk abinda ya samu dayansu kamar ya sami dukkansu ne.

Fayemi ya bada gudunmuwar Naira miliyan 100 ga jihar Borno a madadin NGF don taimakawa al'ummar jihar.

Ya kuma bukaci gwamna Zulum ya rika takatsantsan da rayuwarsa duk da cewa sai lokacin da Allah ya kaddara mutum kwanan sa sun kare zai mutu.

Kimanin sojojin Chadi 1200 da aka tura zuwa Tafkin Chadi na Arewa maso gabashin Najeriya sun koma kasarsu bayan aikin hadin gwiwar da suka yi da sojojin Najeriya ya zo karshe.

A wani labarin, Rundunar 'yan sandan Najeriya a ranar Laraba 30 ga watan Satumba ta gabatar da wasu da ake zargi da aikata fashi da makami, garkuwa da 'yan bindiga da 'yan sanda na musamman masu yaki da 'yan fashi SARS suka kama a jihohi daban-daban.

Mutum bakwai da ake zargin suna da hannu cikin fashin da aka yi wa motar daukan kudi tare da kashe 'yan sanda a jihar Ebonyi a ranar 29 ga watan Yulin 2020 suna cikin wadanda aka yi holen su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel