Mutum na farko da ya warke daga cutar HIV ya rasu sakamakon cutar Cancer

Mutum na farko da ya warke daga cutar HIV ya rasu sakamakon cutar Cancer

- Timothy Ray Brown shine mutum na farko da ya warke daga cutar HIV a duniya

- A ranar Talata, ya rasu sakamakon fama da yayi da cutar cancer ta jini

- Tun a 2008 da ya warke daga HIV, masana kimiyya sun ce za a iya samun maganin cutar

Mutum na farko a duniya daya warke daga cutar HIV, Timothy Ray Brown, ya mutu sakamakon cutar Cancer kamar yadda Bijan Farnoudi, daraktan yada labarai da hulda da jama'a (IAS) na kungiyar masu AIDS ya bayyana.

Brown, wanda aka fi sani da 'Berlin Patient', ya rasu ranar Talata bayan fama da cutar Cancer ta jini na tsawon watanni.

A wata takardar da IAS ta wallafa, Brown ne mutum na farko da ya taba warkewa daga cutar HIV a shekarar 2008.

A watanni 6 na baya,Timothy yayi ta fama da cutar Cancer ta jini wadda ta ratsa kwakwalwarsa da kashin gadon bayansa. Duk da har a lokacin ya rabu da cutar HIV.

"A madadin 'yan kungiyar da shugabanni, IAS na mika sakon ta'aziyyar ta ga matar Timothy, Tim da 'yan uwa da abokan arzikinsa.

"Bayan warkewar Timothy, mun yarda cewa watarana cutar HIV zata samu makari." takardar tace.

Kuma ana cigaba da bincike da nazari, ana fatan za'a samu nasara nan ba da dadewa ba.

KU KARANTA: Hotunan fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya

Mutum na farko da ya warke daga cutar HIV ya rasu sakamakon cutar Cancer
Mutum na farko da ya warke daga cutar HIV ya rasu sakamakon cutar Cancer. Hoto daga @Dailynigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Damfara: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu

A wani labari na daban, Sarkin Kuwait mai shekaru 91 da haihuwa, Sarki Sabah Al-Ahmad Al-Sabah ya rasu ranar Talata a wani asibiti a Amurika.

"Muna bakin cikin sanar da mutuwar Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-jaber Al-Sabah, sarkin Kuwait," inji Sheikh Ali Jarrah Al-Sabah, ministan yada labaran kasar.

An haifi Sheikh Sabah a shekarar 1929, ya rike kujerar ministan harkokin kasashen waje na tsawon shekaru 40, tsakanin 1963 zuwa 2003 daganan ya zama shugaban kasa.

Ya zama sarkin Kuwait a watan Janairu, 2006 bayan rasuwar Sheikh Jabeer Al-Sabah.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel