'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)

'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)

- Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da damke wasu mutum bakwai

- Ana zarginsu da zama gagaruman 'yan fashin da suka addabi jihar Adamawa

- Kwararru ne wurin satar babura da motoci tare da tare jama'a a kan hanyoyi

'Yan sandan jihar Adamawa sun kama wasu 'yan ta'adda 7 da suka addabi kananan hukumonin Girei, Ganye da Mayo-Belwa da ke jihar.

Yan sanda sun kama wasu 'yan fashi 7 da suke addabar jihar Adamawa.

Kakakin 'yan sandan, DSP Suleiman Nguroje, ya sanar da hakan a ranar Talata 29 ga watan Satumba, inda yace 'yan sandan sun kama wadanda ake zargi da fashi a kananan hukumomin Girei, Ganye da SARS.

A yadda Nguroje ya ce, 'yan fashin sun tare motocin haya da babura, inda har suka ji wa mutane da dama ciwo kuma suka kwace musu baburan.

"Bincike ya nuna shedanun 'yan fashin sun hada da Kabiru Muhammed mai shekaru 23, Idris Salisu mai shekaru 42 da Friday Elkanai 23, duk mazauna Wuro-Hausa, Yola South, LG Lafiya dake karamar hukumarLamurde da Dikong dake karamar hukumar Mayo-Belwa duk yan kungiyar mafarauta ne, inda sukaci amanar al'umma.

"Sannan a ranar 27 ga watan Satumba 2020, wasu jaruman 'yan sandan SARS sun samu nasarar kama Sadiq Abdullahi mai shekaru 20, Auwal Bakari 23, Aminu Gidado 23 da Aliyu Abubakar mai shekaru 25 duk mazauna karamar hukumar Mayo-Belwa.

"Sun kwace bindigogi 2, adduna 4, wukake 3 da kayan sojoji da takalmansu," kamar yadda takardar tazo.

Yace 'yan sandan suna cigaba da tabbatar da wadanda akaji wa raunukan na samun kulawa a asibiti, sannan ana rokon jama'a idan sun ga wani da alamar rashin gaskiya suyi gaggawar sanar da 'yan sanda mafi kusa.

'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)
'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Fada a kan saurayi: Budurwa ta yi hayar 'yan daba, sun kashe budurwar saurayinta

'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)
'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)
'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square

'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)
'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

A wani labari na daban, hankula sun tashi sakamakon ganin gawar wani mafarauci a Isuikwuato a jihar Abia.

An tsinci gawar Kelechi Ochu mai shekaru 27 dan Umuasua a karamar hukumar Isuikuato wanda ake zargin an kashe shi yana farauta.

An tsinci gawarsa a dajin Nkwonta, inda aka ga babu wayarsa, babur dinsa da bindigar farautarsa.

A yadda labari ya iso mana, wani dan uwan mamacin, Ochuba Lucky ya ce Ochu mafarauci ne mai rijista da gwamnati, kuma dan karamar hukumar Isuikuato, kuma mafarauta na da damar zuwa wuri-wuri don farauta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel