Nigeria @ 60: Sarauniyar Ingila ta aike wa Buhari da sakon taya murna

Nigeria @ 60: Sarauniyar Ingila ta aike wa Buhari da sakon taya murna

- Mai girma Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth, ta aiko wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakon taya murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai

- Mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Cheif Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a wata wasika da ya fitar a ranar Laraba

- Ya bayyana cewa, sarauniyar Ingilan ta ce tana taya Najeriya murnar cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Birtaniya

Mai girma, Sarauniyar Ingila ta turo sakon taya murna ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan bikin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai da za'ayi ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.

Mai bai wa Shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai, Chief Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wata takardar da ya bayar ranar Laraba a Abuja, inda yace hukumar Birtaniya dake Najeriya.

Kamar yadda sakon yazo, "Ina mai matukar farin cikin taya Najeriya cika shekaru 60 da samun 'yancin kai, ina kuma yiwa Najeriya fatan alheri da fatan wanzuwar farinciki da cigaba."

KU KARANTA: Shugabancin kasa a 2023: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo

Nigeria @ 60: Sarauniyar Ingila ta aike wa Buhari da sakon taya murna
Nigeria @ 60: Sarauniyar Ingila ta aike wa Buhari da sakon taya murna. Hoto daga @Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Harin tawagar Zulum: Rundunar soji na goyon bayan mayar da 'yan gudun hijira gida

A wani labari na daban, daga cikin shagulgulan cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya a Abuja, ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, 2020.

An sanar da hakan a wata takarda da mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa akan yada labarai, Femi Adesina ya sa hannu. Shugaban kasa zai yi jawabin ne bayan anyi faretin zagayowar shekarar.

"Za'a fara nuna jawabin shugaban kasa a tashoshin talabijin da gidajen radiyo bayan an gama fareti karfe 10am daidai, musamman NTA da FRCN," kamar yadda takardar tazo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel