Shugabancin kasa a 2023: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo

Shugabancin kasa a 2023: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo

- Batun wa zai mulka Najeriya bayan saukar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza akala

- Wata kungiyar Yarabawa, IPSC tayi kira akan a bar ibo su mulka Najeriya a 2023

- Kungiyar tace mulkin Najeriya a hannun ibo zai kawo adalci, hadin kai da kuma ba wa kowa hakkinsa

Kungiyar Igbo for President Solidarity Congress (IPSC), wata kungiya ce a kudu maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da bada hadin kai dari bisa dari akan shugabancin dan kudu maso gabas a shekarar 2023.

Ta ce yin hakan ne kadai zai kawo hadin kai a Najeriya.

Shugaban kungiyar, Dr Olukayode OshinAriyo ne yayi wannan kiran a ranar Talata, 29 ga watan Satumba a Ibadan, jihar Oyo.

IPSC ta ce kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya nuna, kudu maso gabas suna da damar rike kujerar shugabancin kasar Najeriya.

Kungiyar tace ayi amfani da NC na 2014, wanda yace kowanne dan kasa zai mulkar Najeriya.

KU KARANTA: Ayyuka 774,000: Jerin sunayen bankuna 6 da za su budewa ma'aikata asusu - FG

Shugabancin kasa a 203: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo
Shugabancin kasa a 203: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo. Hoto daga Daily Sun
Asali: UGC

KU KARANTA: Magu bai amsa abinda ake zarginsa ba, bai roki kwamitin ba - Lauyan Magu

A wani labari na daban, John Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya ce mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance mara sa'a tun farkon shi.

A yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke Benin a ranar Litinin, ya ce ba don salon mulkin ba, da Najeriya bata samu cigaban da ta samu a yanzu ba, The cable ta wallafa.

A yayin jajantawa a kan manyan kalubalen da suka addabi kasa, Oyegun ya ce wadanda ke mulki a yanzu ba su yin kokarin da ya dace kuma hakan ta sa 'yan Najeriya suka sare.

"Al'amura sun yi tsauri. Abinda zan iya cewa shine an gina ginshikin cigabanmu amma kuma mulkin nan babu sa'a," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel