Sojoji sun aike da 'yan ta'adda masu yawa lahira a Tafkin Chadi (Bidiyo)

Sojoji sun aike da 'yan ta'adda masu yawa lahira a Tafkin Chadi (Bidiyo)

- Rundunar sojojin Najeriya sun kai hari cibiyar tsara zirga-zirgan yan ta'addan kungiyar ISWAP a Tafkin Chadi

- Sojojin sun kai harin ne a ranar 29 ga watan Satumba bayan bayanan sirri sun tabbatar da ƴan ta'adda a wurin

- Jiragen yakin NAF ya tarwatsa gine-ginen da mayaƙan ƴan ta'addan da ke ciki tare da lalata makamansu

An kashe ƴan ta'adda da dama sakamakon harin da sojojin saman Najeriya na Operation Lafiya Dole suka kai Tumbuma Baba a Tafkin Chadi inda ƴan ta'addan ISWAP ke amfani da shi a matsayin cibiyar tsara zirga-zirga.

Sojoji sun aike da 'yan ta'adda masu yawa lahira a Tafkin Chadi (Bidiyo)
Sojoji sun aike da 'yan ta'adda masu yawa lahira a Tafkin Chadi (Bidiyo). Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

An kai harin saman ne a ranar 29 ga watan Satumban 2020 a ƙarƙashin shirin atisayen Operation Hail Storm.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

Sojojin sun kai harin ne bayan bayannan sirri sun tabbatar da cewa mayakan ISWAP da dama da shugabannin su sun taru a wasu gidaje a yankin sun shirya kai hari.

Hakan yasa Rundunar sojin ta aike da jiragen saman yaki na NAF da jirage masu saukan ungulu zuwa wurin.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya rantsar da aikin layin dogo na Warri-Itakpe (Bidiyo)

Sun yi nasarar tarwatsa ƴan ta'adda da dama sannan sun lalata gine-ginen ƴan ta'addan.

Kakakin rundunar tsaro Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ta shafin Twitter na hukumar a ranar 30 ga watan Satumba.

A wani rahoton, wasu 'yan bindiga a yammacin ranar Lahadi sun kashe wani dan acaba sun kuma sace shugaban karamar hukumar riko na Kaura a jihar Kaduna, Dr. Bege Katuka.

Daily Trust ta ruwaito cewa an sace shugaban karamar hukumar ne a hanyarsa ta zuwa gonansa kusa da Kidinu, wani karamar gari a Maraban Rido a karamar hukumar Chikun misalin karfe 4 na yamma.

An gano cewa shugaban karamar hukumar ya dauki hayan dan acabar ne ya kai shi gona.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel