Harin tawagar Zulum: Rundunar soji na goyon bayan mayar da 'yan gudun hijira gida

Harin tawagar Zulum: Rundunar soji na goyon bayan mayar da 'yan gudun hijira gida

- Rundunar sojin kasar nan ta tabbatar da cewa tana bada goyon baya ga kudirin Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno

- Duk da harin da 'yan Boko Haram ke kai wa tawagar gwamnan, rundunar ta ce tana goyon bayan kokarinsa na mayar da 'yan gudun hijira gidajensu

- A matsayin rundunar na mai kishin kasa da kuma manyan mayakan ta'addanci, sun ce za su tabbatar da kudirin gwamnan

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana matukar goyon bayan kokarin gwamnatin jihar Borno wurin mayar da 'yan gudun hijira gidajensu a jihar.

Mukaddashin shugaban fannin yada labarai, Sagir Musa, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Premium Times ta wallafa.

Musa, mai mukamin kanal, ya kwatanta kokarin Gwamna Babagana Zulum wurin mayar da 'yan gudun hijira gidajensu da abun yabo kuma abinda ya dace.

Ya ce rundunar sojin Najeriya a matsayinta na mai kishin kasa kuma babbar cibiyar yaki da ta'addancin a yankin arewa maso gabas, za ta tabbatar da cimma burin gwamnan.

Kamar yadda yace, rundunar sojin tana sake jaddada goyon bayanta wurin mayar da 'yan gudun hijirar gidajensu.

KU KARANTA: Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)

Harin tawagar Zulum: Rundunar soji na goyon bayan mayar da 'yan gudun hijira gida
Harin tawagar Zulum: Rundunar soji na goyon bayan mayar da 'yan gudun hijira gida. Hoto daga @GovBorno
Asali: Twitter

KU KARANTA: Magu bai amsa abinda ake zarginsa ba, bai roki kwamitin ba - Lauyan Magu

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce rundunar "Operation Accord" sun kashe yan bindiga 2, sun kama 3 kuma sun kwace makamai da dama a Dajin Kajuru dake karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Shugaban watsa labaran sojoji, John Enenche ya sanar da hakan a ranar Talata a Abuja.

Ya ce an samu yan bindiga da suka samu damar tserewa duk da harbin da suka sha. A cewarsa, lokacin da suka je sintirin, sun kwace carbi 2, da kuma bindigogin yaki 36 da babura 2.

Ya ce, "Duk da dabarar yan ta'addan na tserewa daga harin da rundunar suka kai musu, sai da sojojin suka samu damar kama wasu 3 a kauyen Kujeni.

"Yanzu haka, rundunar ta kewaye kauyukan saboda hana yan bindigar walwala da cigaba da cutar da al'umma."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel