'Yan sanda sun kama wani mutum saboda ya 'kama' abin bauta a Nsukka

'Yan sanda sun kama wani mutum saboda ya 'kama' abin bauta a Nsukka

- Wani mutum Nnajiofor Donatus ya kutsa wurin wani bauta na gargajiya ya kama abin bautar da ya yi ikirarin shine dalilin fitintinu da dama a garin

- Donatus ya yi ikirarin cewa abin bautar ne ya hana shi samun nasara a wurin sana'arsa, ya hana mata samun mijin aure a garin da sauransu

- Daga bisani 'yan sanda sun kama Donatus an kuma karbe abin bautar an kai shi wurin ajiye kayan tarihi da ke Okunere

'Yan sanda a Enugu sun kama wani mutum da ya shiga wani wurin bauta ya kama abin bautar da ya ce ya hana mutanen garin cigaba, ya yi sanadin tabarbarewar kasuwanci tare da hana 'yan mata samun mazan aure.

An kama wani mutum saboda ya 'kama' abin bauta a Nsukka
An kama wani mutum saboda ya 'kama' abin bauta a Nsukka. Hoto: @LindaIkeji
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jawabin rabuwar Najeriya: Dattawan Arewa sun gargadi mataimakin shugaban kasa Osinbajo

Mutumin mai matsakaicin shekaru, Nnajiofor Donatus ya ce wahayi aka masa ya tafi ya cire abin bautar daga inda ya ke.

Ya yi ikirarin cewa abin bautar ne ya janyo talauci a garin Ibeku Opi inda ya kara da cewa kasuwancinsa na sayar da zuma ta rushe a Anambra ya dawo gida ba shi da komai.

Vanguard ta ruwaito cewa mutane sun ji tsoron mutumin da suka ga ya dakko abin bautar, sun kuma lura yana nuna wasu halaye da ba a saba gani ba domin ya kan yi haushi irin na karnuka idan an kusance shi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

Rahotanni sun ce ya yi barazanar kai wa mutan hari a lokacin da suka yi yunkurin hana shi shiga dakin ajiye kayan tarihi na Okunere da ke cocin St. Theresa domin ceto mutanen garin Ibeku Opi daga tsaffin da abin bautar ke da shi.

Mai kula da cocin St. Theresa da ke Nsukka Rabaran Fada Mathew Eze wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce kamata ya yi Nnajiofor ya tuntubi shugabannin cocin su shiga wurin bautar su dauka su kai wurin ajiyar kayan tarihi na Okunere inda ake ajiye sauran kayan tarihin.

A wani labrin daban, wasu fusatattun matasa a ranar Talata sun kai wa hadimin gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar da wasu jami'an gwamnatin jihar hari.

Channels Television ta ruwaito cewa wadanda aka kai wa harin sune mashawarcin gwamnan na musamman kan ayyukan cigaban garuruwa, Mista Hamza Mohammed da wasu jami'an hukumar bada agajin gaggawa na jihar SEMA.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel