Magu bai amsa abinda ake zarginsa ba, bai roki kwamitin ba - Lauyan Magu

Magu bai amsa abinda ake zarginsa ba, bai roki kwamitin ba - Lauyan Magu

- Lauya mai kare dakataccen shugaban EFCC, Wahab Shitu, ya yi karin bayani a kan rade-radin da ake na cewa Magu ya amsa laifin da ake zarginsa

- Shitu ya tabbatar da cewa, wanda yake karewa bai amsa laifin da ake tuhumarsa ba kuma bai bada hakuri ba

- Ya kara da cewa, har a halin yanzu kwamitin Ayo Salami na fadar shugaban kasa yana bincikarsa kuma ya gurfana a ranar Juma'a

Wahab Shitu, lauya mai kare shugaban EFCC, Ibrahim magu, ya ce wanda yake karewa bai amsa laifin da ake zarginsa ba.

A wata magana ta daban, an yada cewa Magu ya ce da kwamitin binciken ya firgita a matsayinsa na shugaban EFCC kuma ya nemi yafiya.

Kamar yadda lauyan ya ce, tsohon shugaban EFCC bai amince da rashawar da ake zarginsa dashi ba, kuma bai roki gafarar kowa ba.

"Babu ranar da Magu ya taba amincewa da laifin da ake zarginsa dashi," a cewar Shitu.

"Wani lauyan da muke aiki tare ya tambayeni ko ina tunanin kotu zata yi wa wanda nake karewa adalci.

"Na amsa mishi da cewa, inada yakinin cewa za a yi mishi adalci, tunda nasan ba shi da laifi," Shitu ya kara da cewa.

Shitu yace, kamar yadda yan Najeriya ke jiran Ayo Salami, haka ya shige gaba wurin yiwa al'amarin Magu adalci.

Tsohon shugaban EFCC ya bayyana gaban kwamitin a ranar juma'a don kare kansa.

KU KARANTA: Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani

Magu bai amsa abinda ake zarginsa ba, bai roki kwamitin ba - Lauyan Magu
Magu bai amsa abinda ake zarginsa ba, bai roki kwamitin ba - Lauyan Magu. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)

A wani labari na daban, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu, ya musanta zarginsa da ake da karbar cin hanci.

Wannan takardar ta fito ne bayan da dakataccen shugaban EFCC ya fara kare kansa a bisa zarginsa da ake yi da watanda da kudade da kadarorin da aka karbo na gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel