Matasa sun bankawa ofishin yan sanda da na Immigration wuta a jihar Katsina

Matasa sun bankawa ofishin yan sanda da na Immigration wuta a jihar Katsina

- Rikici ya barke tsakanin matasa masu zanga-zanga da Jami’an tsaro

- An yi rashin ran akalla mutum daya a rikicin

- Masu zanga-zangan sun afkawa matafiyan cake wucewa a hanyar Jibia a lokacin

Wasu fusatattun matasa a garin Daddara dake karamar hukumar Jibiya na jihar Katsina masu zanga-zanga kan rashin isasshen tsaro da yawaitan hare-haren yan bindiga sun bankawa ofishin yan sanda da na jami’an shiga da fice (Immigration) wuta.

Wani ganau ba jiyau ba, ya bayyanawa The Nation cewa matasan sun kona tayoyin mota kuma sun tare hanyoyin shiga Jibiya daga Katsina.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Isah Gambo, ya tabbatar da hakan. Ya ce an damke 43 cikin matasan da ake zargi.

KU KARANTA: Sayar da NNPC zamu yi ba shafeta ba - Ministan Mai

Yace: “Hukumar ta samu rahoton cewa wasu fusatattun matasa daga kauyen Daddara, karamar hukumar Jibiya sun fito kwansu da kwarkwatansu sun gudanar da zanga-zanga.”

“An kawo rahoton cewa matasan sun tare hanyar Katsina zuwa Jibiya, daidai kauyen Daddara inda suka lalata motocin jami’an tsaro da na daidaikun mutane masu wucewa a hanyar.”

“Hakazalika sun kona ofishin yan sandan dake Daddara, ofishin hukumar Immigration dake Danmasani, motar sintirin yan sanda, motar wani dan sanda kirar Volkswagen Gulf III, bindigogin AK47 na jami’an kare iyaka biyu, bindiga AK47 da karamar bindiği da yan sanda.”?

“Bugu da kari, matasan sun fasa gilashen motocin matafiya da dama da suka bi ta hanyar.”

“Sakamakon haka, hukumar ta tura jami’an PMF hajen kuma suka samu nas arar damke mutane arba’in da uku (43) cikinsu.”

KU KARANTA: Ana saura kwanaki 11 zabe, Buhari na son baiwa jihar Ondo N7bn

Yace tuni an kwantar da kuran kuma za’a hukunta dukkan wadanda aka kama da laifi saboda hakan ya zama izina ga wasu.

Ya bayyana cewa mutum daya ya rasa rayuwarsa kuma bincike ya nuna cewa wasu yan sumoga ne suka dauki nauyin matasan domin kawar da jami’an dake tsaron iyakar Najeriya.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ga majalisar dokokin tarayya makon gobe, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya laburta.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel