Ana saura kwanaki 11 zabe, Buhari na son baiwa jihar Ondo N7bn

Ana saura kwanaki 11 zabe, Buhari na son baiwa jihar Ondo N7bn

- Mambobin majalisar dokokin tarayya sun koma bakin aiki bayan dogon hutu

- Yan majalisar sun fara aikinsu da wasikun da Buhari ya aike musu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokokin tarayya ta bash damar baiwa jihar Ondo, Bayelsa,Cross River, Osun da Rivers, kudi N148bn kan wasu gine-ginen titunan gwamnatin tarayya da suka yi.

Shugaban kasan ya gabatar da bukatarsa ne ta wasikar da ya aikewa kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, kuma aka karanta a zauren masjalisa radar Talata.

Daga cikin jihohin da za’a baiwa kudi, jihar Ondo da za’a guadar da zabe mano gobe zata samu bilyan bakwai.

KU KARANTA: Sayar da NNPC zamu yi ba shafeta ba - Ministan Mai

Za ku tuna cewa a 2019, majalisar ta baiwa shugaba Buhari daman baiwa jihar Kogi bilyan goma, ana saura kwanaki goma zaben jihar.

Hakan ya faru duk da cewa yan majalisar PDP sun nuna rashin amincewarsu da hakan kuma suka bukami a dakatar har sai bayan zaten jihar.

Amma ba’a yi hakan ba, an ba Kogi kudin.

Saurarin karin bayani anjima…

KU KARANTA: Matasa sun bankawa ofishin yan sanda da na Immigration wuta a jihar Katsina

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ga m ajalisar dokokin tarayya makon gobe, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya laburta.

Ya bayyana hakan cikin jawabin maraba da zuwan da yayiwa Sanatoci bayan watanni da suka kwashe suna hutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel