Rundunar soji sun halaka 'yan bindiga 2, sun cafke 3 a Kaduna - DHQ

Rundunar soji sun halaka 'yan bindiga 2, sun cafke 3 a Kaduna - DHQ

- Hedkwatar tsaro ta yaba wa rundunar "Operation Accord" akan nasarorin kashe yan bindiga 2, da kama 3 tare da kwashe makamansu

- Rundunar sojojin da taimakon yan sa kai sun ratsa cikin Dajin Kajuru inda suka kashe yan ta'adda har da ji wa wasu raunika

- Yanzu haka rundunar ta zagaye Dajin Kajuru don hana yan ta'addan walwala da cigaba da cutar da al'umma

Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce rundunar "Operation Accord" sun kashe yan bindiga 2, sun kama 3 kuma sun kwace makamai da dama a Dajin Kajuru dake karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Shugaban watsa labaran sojoji, John Enenche ya sanar da hakan a ranar Talata a Abuja.

Enenche yace, an samu wannan nasarar lokacin da rundunar ta fita rangadi tare da yan sa kai.

Ya ce an samu yan bindiga da suka samu damar tserewa duk da harbin da suka sha.

A cewarsa, lokacin da suka je sintirin, sun kwace carbi 2, da kuma bindigogin yaki 36 da babura 2.

Ya ce, "Duk da dabarar yan ta'addan na tserewa daga harin da rundunar suka kai musu, sai da sojojin suka samu damar kama wasu 3 a kauyen Kujeni.

"Yanzu haka, rundunar ta kewaye kauyukan saboda hana yan bindigar walwala da cigaba da cutar da al'umma."

"Hukumar sojojin tayi na'am da kokari da jajircewar rundunar, inda take kara basu kwarin guiwa akan cigaba da ragargazar yan ta'adda a fadin Najeriya.

"Don haka ana neman hadin kan al'umma wurin bada bayanai da zasu taimaka wurin damkar yan ta'addan dake wurarensu," a cewarsa.

KU KARANTA: Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani

Rundunar soji sun halaka 'yan bindiga 2, sun cafke 3 a Kaduna - DHQ
Rundunar soji sun halaka 'yan bindiga 2, sun cafke 3 a Kaduna - DHQ. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

KU KARANTA: Ba dai a ma'aikata ta ba: Sadiya Farouq ta yi martani a kan ikirarin ICPC

A wani labari na daban, wasu mayakan ta'addancin Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a Banki.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta wallafa, ta bayyana hotunan mayakan ta'addancin tare da iyalansu da suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Mayakan ta'addancin tare da iyalansu sun mika kansu ne ga bataliya ta 155 da ke Banki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel