Rikicin APC a Ekiti: El-Rufai, Wase da Okorocha sun jagoranci kwamitin sulhu

Rikicin APC a Ekiti: El-Rufai, Wase da Okorocha sun jagoranci kwamitin sulhu

- Kwamitin kwantar da rikici jam'iyyar APC ta wakilta mutane 6 suje sasanci a jihar Ekiti

- Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci yan kwamitin kwantar da rikici

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ne Shugaban kwamitin, kuma ana rokon hadin kan yan jam'iyya

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jagoranci kwamitin kwantar da rikicin jam'iyyar APC.

Inda ya shiga cikin mutum 6 da aka zaba wurin kwantar da rikici da ta taso a jihar Ekiti. Malam Nasir Ahmad El-Rufai ne shugaban kwamitin, Channels Tv ta wallafa.

An bayyanar da hakan a wata takarda da sakataren jam'iyyar, Yekini Nabena yasa hannu a kai ranar Talata.

Ya kara da cewa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya rantsar da kwamitin kula da jam'iyyar APC da kwantar da rikici a babban ofishin jam'iyyar dake Abuja, kuma ya roki yan jam'iyyar su basu hadin kai.

A yadda takardar tazo, "Kamar yadda kwamitin kwantar da tarzomar jam'iyyar APC ta tanadar, muna rokonku da ku bada cikakken hadin kai don kwantar da duk wata rikici da fadace-fadacen da ke tsakanin yan jam'iyyar mu.

"Muna kira ga yan jam'iyya da kuma shugabannin jihar Ekiti da su hada kai da Gwamna Nasir El-Rufai wurin kwantar da rikicin da ta kunno kai a jihar Ekiti."

KU KARANTA: Durkusawar budurwa a gaban saurayi don karbar tayin aure ya janye cece-kuce

Rikicin APC a Ekiti: El-Rufai, Wase da Okorocha sun jagoranci kwamitin sulhu
Rikicin APC a Ekiti: El-Rufai, Wase da Okorocha sun jagoranci kwamitin sulhu. Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

KU KARANTA: Ba dai a ma'aikata ta ba: Sadiya Farouq ta yi martani a kan ikirarin ICPC

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yana fatan babu wani dan Najeriya da zai wahala koda a wacce jam'iyya yake.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne lokacin da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya raka mataimakinsa, Philip Shuaibu da wasu yan jam'iyyarsu don godiya ga shugaban kasar a Abuja.

Shugaba Buhari ya sha alwashin kokarta wa wurin ciyar da al'umma gaba a bisa gaskiya da amana. Sannan ya roki jama'a dasu dage wurin bada hadin kai ga gwamnati don samun cigaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel