'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

- Ƴan bindiga sun kai hari a garin Wasugu da ke ƙaramar hukumar Wasagu Danko na jihar Kebbi

- Sun kashe mutum ɗaya, sun raunata raunata uku sun kuma yi awon gaba da wasu

- Kawo yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalan wadanda suka sace ba domin neman biyan kuɗin fansa

An kashe mutum ɗaya an kuma yi garkuwa da wasu bakwai a lokacin da ƴan bindiga suka kai hari garin Wasagu da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu na jihar Kebbi.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama
'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama. Hoto: @SaharaReporters
Source: Twitter

Yan bindigan sun afka garin na Wasugu a daren ranar Lahadi inda suka rika buɗe wa gidaje da mutane wuta.

Wani ganau, da ya yi magana da SaharaReporters ya ce mutum uku sun jikkata sakamakon harin.

DUBA WANNAN: Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun marawa Obaseki baya saboda 2023 - Kakakin Tinubu

"Sun afka garin misalin ƙarfe 7 na dare suka fara harbe-harbe, mutum uku sun samu munanan rauni.

"Ɗaya daga cikin mutane ukun ya mutu yayin da sauran biyun sunan can suna karɓar magani a Cibiyar Lafiya ta Wasugu.

"Yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane a garin mu yayin da wasu suka ruga gidajensu suka rufe kofofi.

"Bayan harin, mun gano cewa sun sace mutane biyar," a cewar wani mazaunin garin Aliyu.

KU KARANTA: 'Yan sintiri ga FG: A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga

Ya ce duk da cewa a yanzu an samu lafiya a garin, mutane da dama suna zaman fargaba ne.

Ya ƙara da cewa har yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalan wadanda suka sace ba kan batun biyan kudin fansa.

A wani labarin daban da Legit.ng ta wallafa, mutane da dama sun bace sakamakon fadawa cikin rafin Epe da wata mota ta yi daga gadar Berger a jihar Legas.

The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma'a 25 ga watan Satumban 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel