Da duminsa: Buhari ya rantsar da aikin layin dogo na Warri-Itakpe (Bidiyo)

Da duminsa: Buhari ya rantsar da aikin layin dogo na Warri-Itakpe (Bidiyo)

- Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin ginin layin dogo na Warri-Itakpe

- Shugaban kasar ya kaddamar da aikin ne ta amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti

- Legit.ng ta ruwaito cewa an saka sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a tashan Agbor

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata 29 ga watan Satumban ya kaddamar da aikin layin dogo na takpe-Ajaokuta-Agbor-Warri ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti.

An yi bikin ne a tashan jirgin kasa na Agbo inda aka saka wa tashar sunan tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan.

Da ya ke jawabi wurin taron, Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su tallafawa gwamnatinsa bisa kokarin samar da gine-gine.

Buhari ya rantsar da aikin layin dogo na Warri-Itakpe
Buhari ya rantsar da aikin layin dogo na Warri-Itakpe
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya Pete Edochie martani

Ya kuma sanar da cewa akwai bukatar a rika kula da ayyukan da gwamnati ke yi a garurruwa.

Kazalika, shugaban kasar ya bukaci masu ruwa da tsaki a fanin karafa da noma su yi amfani da damar da ta samu don inganta ayyukansu.

Bayan farfado da masana'antar karafa ta Ajaokuta, Shugaba Buhari ya taya ministan sufuri, Rotimi Ameachi da mutanen garin murnar kammala aikin.

Tun a shekarar 1987 aka fara bada kwangilar aikin layin dogon. A 2009, gwamnatin Goodluck Jonathan ta farfado da aikin da ware kudi Naira biliyan 33 tare da yin kwaskwarima a tsarin aikin.

KU KARANTA: 'Yan sintiri ga FG: A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga

Bayan canjin gwamnati a 2015 aka yi watsi da aikin bayan an kammala kashe 70 cikin 100 na aikin saboda rashin kudi.

A 2017, gwamnatin Buhari ta sanar da cewa za ta ware kudi Naira biliyan 72 don farfado da aikin Itakpe - Warri.

Bayan kammala aikin, zai sada jihohi uku da suka hada da Kogi, Edo, Delta sai kuma babban birnin tarayya, Abuja.

A wani rahoton, dan majalisa mai wakiltar Oyo ta Arewa, Sanata Abdulfatai Buhari ya ce zai goyi bayan jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu idan ya nuna sha'awar fitowa takarar shugabancin kasa a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin hirar da ya yi da wani dan jarida, Edmund Obilo a ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel