Mutumin da ya dauka alwashin sanya wa dan shi Buhari ya sanya Aisha bayan an haifa masa mace

Mutumin da ya dauka alwashin sanya wa dan shi Buhari ya sanya Aisha bayan an haifa masa mace

- Malam Zakariyya Aliyu mutum ne da ke matukar kaunar shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Tun matarsa na dauke da juna biyu ya sha alwashin saka wa jinjirin suna Buhari

- Amma sai Allah ya kawo diya mace, lamarin da yasa ya sanya wa diyar suna Aisha

Wani mutum mai suna Malam Zakariyya Aliyu, ya sanya wa diyarsa suna Aisha domin girmamawa ga shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Aliyu dan asalin garin Kontagora ne daga jihar Neja wanda ya dauka alkawarin sanya wa dansa namiji suna Buhari idan Allah ya sauka mai dakinsa lafiya.

Amma kuma, bayan an sanar da shi cewa matarsa ta haifa diya mace, sai ya yanke shawarar karrama shugaban kasar.

Ya saka wa yarinyar suna Aisha saboda wannan ne sunan matar shugaban kasar.

KU KARANTA: Kanuri: Al'ada, addini, aure, abinci da tsatson babbar kabilar

Mutumin da ya dauka alwashin sanya wa dan shi Buhari ya sanya Aisha bayan an haifa masa mace
Mutumin da ya dauka alwashin sanya wa dan shi Buhari ya sanya Aisha bayan an haifa masa mace. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba dai a ma'aikata ta ba: Sadiya Farouq ta yi martani a kan ikirarin ICPC

A wani labari na daban, bidiyon wata karamar yarinya ya bar jama'a da dama baki bude sakamakon hazaka da kaifin basirarta wurin nuna kaunar iyayenta.

A bidiyon mai tsayin minti uku, an ga yarinyar tana bai wa iyayenta shawarwarin zamantakewar aure.

Tiana ta bada wannan shawarar ne domin taimaka wa iyayenta wadanda suka rabu kuma kullum suke fada. Abinda yarinyar karama take bukata shine iyayenta su zama abokan juna, su daina fada.

"Mama, kin shirya zama kawarsa? Ina son komai ya lafa, kin ji?" ta tambaya mahaifiyarta.

Kamar yadda hazikar yarinyar tace, abinda take so shine ganin farin ciki a tattare da su ba fada kullum ba.

"Ina kokarin ganin kun zama nagari. Bana son ganin ki da mahaifina kuna fada, ba zan iya maye gurbinku da kowa ba. Ku sasanta junanku," tace.

Tiana ta yi kira ga iyayenta da su ajiye dukkan makaman rikicinsu, sannan su rungumi zaman lafiya a tsakaninsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel