Gwamnatin tarayya ta bada hutun ranar 1 ga Oktoba

Gwamnatin tarayya ta bada hutun ranar 1 ga Oktoba

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ayi hutun ranar 'yancin kai wato 1 ga watan Oktoba a ranar Alhamis

- Gwamnatin ta taya 'yan Najeriya murnar cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai da ta ce babban abin ayi shagali ne sai dai za a takaita bukukuwan saboda annobar korona

- Sanarwar da ta fito daga ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ta tunatar da 'yan Najeriya game da muhimmancin hadin kai da aiki tare

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar 'yancin Najeriya. Najeriya za ta cika shekaru 60 da samun 'yanci a ranar Alhamis.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya inda ya taya dukkan 'yan Najeriya murnar zagayowar ranar.

Gwamnatin tarayya ta bada hutun ranar 1 ga Oktoba
Gwamnatin tarayya ta bada hutun ranar 1 ga Oktoba. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 30 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

Ya kuma tabbatar musu cewa gwamnati mai ci yanzu ta mayar da hankali domin ganin ta inganta walwala da jin dadinsu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kazalika, ministan ya ce cika shekaru 60 da samun 'yanci babban lamari ne da ya dace ayi murna amma saboda annobar korona za a takaita irin bukukuwan da za ayi.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren dindindin na ma'aikatar harkokin cikin gida Georgina Ehuriah.

KU KARANTA: Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya Pete Edochie martani

A cewar sanarwar, ministan ya jinjinawa 'yan Najeriya bisa nasarorin da suka samu a bangarorin tattalin arziki, ilimi, kirkire-kirkire da sauransu.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa Aregbesola na cewa, "Duk da cewa cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai abin ayi shagali ne sosai, hakan ba zai yiwu ba saboda barazanar annobar korona saboda haka za a takaita bukukuwan."

Ta kara da cewa, "A yayin da na ke taya 'yan Najeriya murna, ina tunatar da su cewa iyayen mu da suka kafa kasar sun hada kai domin samun 'yancin kasar duk da banbancin addini, kabila da harshe tsakaninsu."

A wani rahoton, Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel