Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)

Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)

- Matashi mai shekaru 28 dan asalin kasar Uganda ya kashe iyayensa, matarsa da kuma kanwar matarsa a ranar Alhamis da ta gabata

- Bayan kashesu da yayi, ya boye na kwanaki biyu amma daga bisani ya mika kansa ga 'yan sandan yankin

- Ya ce iyayensa sun bashi wani fili a kwari wanda ba zai iya gina gida a kai ba, lamarin da yasa yayi aika-aikar

Wani matashi mai shekaru 28 wanda ake zargi da kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa a yankin Kisoro da ke yammacin Uganda, ya mika kansa ga 'yan sanda a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba.

Wanda ake zargin mai suna Gerald Ndikumukiza, mazaunin kauyen Kageyo da ke Busengo a ranar Alhamis da ta gabata, ya kashe matarsa mai shekaru 26 mai suna Maserina Mujawimana.

Ya kashe mahaifinsa mai suna Deogratious Sebitama mai shekaru 80, mahaifiyarsa mai shekaru 75 mai suna Bonconsira Nyiraguhirwa kafin ya kashe kanwar matarsa mai shekaru 20 mai suna Joan Nyiramahoro.

Bayan aikata laifin, Ndikumukiza ya boye amma ya bar wata wasika a inda yayi laifin inda ya rubuta, "Abinda kuke son gani."

Wanda ake zargin dan asalin yankin Masaka ne inda yake aiki a matsayin lebura, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan yankin Kigezi, Elly Maate, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce wanda ake zargin ya mika kansa ga 'yan sandan yankin Kisoro kuma ya sanar da jami'an tsaro cewa yana tsoron kada a banka masa wuta.

Maate ya kara da cewa, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa da kanshi ya kashe iyayensa, matarsa da kuma kanwar matarsa a kan rikicin fili. Ya ce sun bashi filin da ba zai iya gina gida a kai ba.

Wanda ake zargin ya ce duk da Masaka da ya tafi domin neman kudi, bai samu ba, hakan ce ta sa ya kashe 'yan uwansa saboda fushi.

Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)
Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Kanuri: Al'ada, addini, aure, abinci da tsatson babbar kabilar

Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)
Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)
Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Sarautar Zazzau: Tsaro ya tsananta a gidan Yariman Zazzau, Mannir Jaafaru

A wani labari na daban, kamar yadda wani mawaki ya wallafa ranar Asabar, 26 ga watan Satumba, wata Chinyere Ezeji ta ce motarsu ta tsaya a wuraren layin Amala/Eziama ranar Juma'a.

Sai suka dakata wurin bakaniken kan hanyar Nkwola-Eziama, mai suna Chukwudi don ya gyara musu motar.

Bayan ya tattaba motar, sai yace bari ya zagaya da ita don ya tabbatar ko gyaran yayi, daga nan ba'a sake ganinshi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel