Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani

Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani

- Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, Tolu Ogunlesi, ya caccaki Shehu Sani

- Tolu Ogunlesi ya bukaci tsohon sanatan Kaduna ta tsakiyan da ya fara yajin aikinsa da kansa tun da TUC da NLC ta fasa

- Hadimin ya yi wannan martani ne bayan da Shehu Sani yace ya shirya yajin aiki amma TUC da NLC sun fasa

Tolu Ogunlesi, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna da ya fara yajin aikinsa.

Tsohon sanatan ya wallafa hoto a ranar Lahadi a Twitter, inda yace yana shirin fara yajin aiki, amma dai hakan bai tabbata ba.

Bayan taron gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago a sa'o'in farko na ranar Litinin, NLC da TUC sun dakatar da fara yajin aiki wanda suka ce babu dadewa za su shiga.

NLC da TUC sun nemi shiga yajin aikin domin nuna rashin aminta da karin kudin wutar lantarki da na man fetur.

A martanin da hadimin shugaban kasar yayi, Ogunlesi ya bukaci sanatan da ya shirya yajin aiki da kansa domin cika burinsa.

"Abu daya dai da na sani shine, za ka iya shirya naka yajin aikin," Ogunlesi yace.

Tsohon sanatan ya kwatanta hadimin shugaban kasar da zama rigimamme.

"Mallam Alhaji Tolu Ogunlesi, shugaban rigimammun fadar shugaban kasa," Sani yace a martaninsa.

KU KARANTA: ICPC ta bankado inda aka yi da N2.67 biliyan ta ciyar da 'yan makaranta

Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani
Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani. Hoto daga @Thecable
Source: Twitter

KU KARANTA: Kanuri: Al'ada, addini, aure, abinci da tsatson babbar kabilar

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai sa ran gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kasa nan kusa.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe iyakokin kasa a watan Oktoba 2019 saboda hana shigowa da kaya da makamai Najeriya, da kuma kiyaye kasuwancin cikin kasa.

Shuwagabannin kasashe kamar Ghana da jamhuriyar Benin sunyi ta rokon shugaban kasa akan ya taimaka ya bude iyakar, amma ya runtse idanunsa yace sam ba zai bude ba har sai kwamitin da ta zartar da rufewar ta duba lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel