An sace shugaban karamar hukuma a hanyarsa ta zuwa gona a Kaduna

An sace shugaban karamar hukuma a hanyarsa ta zuwa gona a Kaduna

- 'Yan bindiga sun kashe dan acaba sannan suka yi yi awon gaba da shugaban karamar hukuma a Kaduna

- 'Yan bindigan sun sace Dr Bege Katuka, shugaban riko na karamar hukumar Kaura ne a yammacin ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa gona

- Majiyoyi daga jam'iyyar APC sun tabbatar da sace shi amma rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ba suyi karin bayani ba

An sace shugaban karama a hanyarsa ta zuwa gona a Kaduna
An sace shugaban karama a hanyarsa ta zuwa gona a Kaduna. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya jajantawa Zulum bisa harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa a Borno

Wasu 'yan bindiga a yammacin ranar Lahadi sun kashe wani dan acaba sun kuma sace shugaban karamar hukumar riko na Kaura a jihar Kaduna, Dr. Bege Katuka.

Daily Trust ta ruwaito cewa an sace shugaban karamar hukumar ne a hanyarsa ta zuwa gonansa kusa da Kidinu, wani karamar gari a Maraban Rido a karamar hukumar Chikun misalin karfe 4 na yamma.

An gano cewa shugaban karamar hukumar ya dauki hayan dan acabar ne ya kai shi gona.

Majiyoyi daga jam'iyyar All Progressive Congress (APC) sun tabbatar da sace shi. Sun shaida wa majiyar Legit.ng Hausa cewa sun yi kokarin tuntubarsa a waya amma ba su same shi ba.

KU KARANTA: Mutum 30 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

"Lamarin ya faru ne misalin karfe 4 zuwa 5 na yammacin ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa gona. Ya bar motarsa a wani wuri ya dauki dan acaba ya kai shi gonarsa amma a hanya 'yan bindiga suka kai musu hari.

"Sun harbe dan acaban ya mutu yayin da suka yi awon gaba da shugaban karamar hukumar. Muna zargin tun daga wani wuri suka biyo shi domin mutanen nan unguwar ba su san shi ba," a cewar wani majiya.

Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan da Kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ba su amsa wayarsu ba.

A wani rahoton, an kashe jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, a daren ranar Laraba yayin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da dilalan bindiga a kauyen Kalong da ke karamar hukumar Shendam ta jihar Plateau.

Daily Trust ta ruwaito cewa sunan jami'in da aka kashe Barista Mukhtar Moddibo dan asalin karamar hukumar Misau daga jihar Bauchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel