'Yan sintiri ga FG: A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga

'Yan sintiri ga FG: A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga

- Kungiyar 'yan sintiri ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) ta ce za ta iya kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga idan an bata dama

- Kungiyar da VGN ta yi kira ga gwamnatin tarayya musamman Majalisar Tarayya su yi gaggawar amincewa da kudirin kafa 'yan sandan unguwanni

- Kungiyar ta bayyana wannan ne yayin wani tattaki da ta gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin

Wasu 'yan Najeriya da ke aikin samar da tsaro a garuruwansu karkashin kungiyar 'Vigilante Group of Nigeria (VGN)' sun bukaci gwamnatin tarayya ta basu damar bada gudunmawarsu wurin yaki da rashin tsaro.

Sun yi wannan kirar ne yayin wata tattaki na awa biyu da suka yi don nuna goyon baya ga 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da aka yi a Abuja a ranar Litinin kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Buhari ya jajantawa Zulum bisa harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa a Borno

A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga - 'Yan sintiri ga FG
A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga - 'Yan sintiri ga FG. Hoto @Vanguardngr
Source: Twitter

'Yan sintirin sun ce suna neman a basu aiwatar da tsarin samar da tsaro a unguwanni domin karfafa tsaro na cikin gida.

Sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin kafa 'yan sandan unguwanni da na 'yan sintiri inda suka ce a shirye suke su kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga da zarar an amince da kudirin.

Kakakin VGN Mukhtr Dahiru ya ce, "Samar da tsaro hakki ne da ya rataya a kan dukkan mu baki daya.

"Saboda haka, muna kokarin ganin an aiwatar da tsarin samar da tsaro a unguwanni ne domin inganta tsaro a kasar.

KU KARANTA: Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya Pete Edochie martani

"Hakan yasa a shirye muke domin taimakawa hukumomin tsaro domin kawo karshen ta'addanci da 'yan bindiga da gwamnati ta sani.

"A shirye muke mu tabbatar da zaman lafiya a unguwannin mu wadda hakan zai taimakawa tattalin arzikin mu ya habbaka hakan ma zai taimaka wurin samar da tsaro.

"Saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayya, musamman Majalisar Tarayya su taimaka a saka hannu kan kudirin kafa 'yan sandan unguwanni ta zama doka."

Sun fara tattakin ne daga Ishaya Shekari Crescent, Gwarimpa Estate suka kare a Unity Fountain da ke Maitama.

A wani labarin, mutane da dama sun bace sakamakon fadawa cikin rafin Epe da wata mota ta yi daga gadar Berger a jihar Legas.

The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma'a 25 ga watan Satumban 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel