Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu (Hotuna)

Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu (Hotuna)

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya gana da iyalan 'yan sanda da 'yan JTF da suka rasu yayin harin da 'yan ISWAP suka kai wa tawagarsa

- Zulum ya yi wa iyalan wadanda suka rasu, rundunar 'yan sanda da 'yan Najeriya ta'aziyya tare da alkawarin tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa

- Gwamnan ya kuma tafi asibiti domin duba mutum takwas da suka jikkata sakamakon harin da suka hada da 'yan sanda da 'yan JTF

Gwamnan Borno Babagana Zulum ya ziyarci iyalan 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri da ke tallafawa dakarun gwamnati wato civilian JTF da yan ta'adda suka kai wa hari a ranar Juma'a a hanyarsu ta zuwa Baga.

Zulum ya ziyarci hedkwatan 'yan sanda na jihar Borno da ke Maiduguri inda iyalan wadanda suka rasu suka taru domin tarbansa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya Pete Edochie martani

Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu
Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu. Hoto: @Thecableng
Asali: Twitter

"Na zo nan ne domin yi muku 'yan uwan mu jaje bisa rasuwar 'yan sandan mu. Abinda ya faru abin bakin ciki ne.

"Ina addu'ar Allah ya gafarta musu ya yafe musu kurakurensu ya kuma baku ikon jure rashi, wannan babban rashi ne gare mu baki daya," inji Zulum.

"Abin bakin ciki ne sosai kuma lamarin ya min ciwo sosai.

"Sai dai ku sani sun mutu a matsayin jarumai da iyalansu za suyi alfahari da su duk da cewa ba muyi fatan hakan ya faru ba," a cewar Zulum.

KU KARANTA: Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun marawa Obaseki baya saboda 2023 - Kakakin Tinubu

Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu
Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu. Hoto: @Thecableng
Asali: Twitter

Gwamnan ya sanar da cewa gwanatin Borno za ta bawa iyalan wadanda suka rasu tallafi sai dai bai bayyana abinda za ayi musun ba 'don gudun kada ayi tsammanin yana kwatantan tallafin da rayukan da aka rasa ne'

"Ina son yi wa rundunar 'yan sandan jihar Borno, Kwamishina da Sufeta na 'yan sanda da sauran 'yan Najeriya ta'aziyya bisa abin bakin cikin da ya faru," in ji Zulum.

Gwamnan ya kuma ziyarci Asibitin Kwararru da ke Maiduguri domin duba wadanda suka jikkata sakamakon harin da halin yanzu suke karbar magani a asibiti.

Shugaban asibitin, Dr Laraba Bello ta fadawa gwamnan cewa mutum takwas aka kawo da suka kunshi 'yan sanda da 'yan JTF. An yi wa biyar magani an sallame su yanzu saura uku suna samun sauki.

Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu
Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu. Hoto: @Thecableng
Asali: Twitter

Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu
Harin Baga: Zulum ya ziyarci iyalan jami'an tsaron da suka rasu. Hoto: @Thecableng
Asali: Twitter

A wani rahoton, an kashe jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, a daren ranar Laraba yayin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da dilalan bindiga a kauyen Kalong da ke karamar hukumar Shendam ta jihar Plateau.

Daily Trust ta ruwaito cewa sunan jami'in da aka kashe Barista Mukhtar Moddibo dan asalin karamar hukumar Misau daga jihar Bauchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel