An cafke mata da miji da mutane biyu dauke da kokon kan mutum a Ogun

An cafke mata da miji da mutane biyu dauke da kokon kan mutum a Ogun

- Rundunar yan sandan jihar Ogun, ta kama wasu mutane hudu bisa zargin samunsu da kokon kan mutum

- Ta kama su ne bayan bayanai da ta samu cewa suna nan suna haka wani kabari da basu da nasaba da mamacin

- Bayan kama su an gano cewa za su yi asiri ne da kokon kan gawar da suka cire

Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun, ta kama wasu mutane hudu bisa zargin samunsu da kokon kan mutum, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mista Abimbola Oyeyemi, kakakin yan sandan jihar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abeokuta a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

Oyeyemi ya bayyana cewa an kama masu laifin da ake zargi, wadanda aka sakaya sunayensu a ranar 25 ga watan Satumba.

Ya ce ofishin yan sandan Odogbolu ta samu wani bayani cewa wasu mutane na hako kabari da kudirin cire gawar wani da baya da nasaba da su.

KU KARANTA KUMA: APC ta tafka babbar asara a Kwara: Kotu ta soke nasarar dan majalisa, ta ba PDP

An cafke mata da miji da mutane biyu dauke da kokon kan mutum a Ogun
An cafke mata da miji da mutane biyu dauke da kokon kan mutum a Ogun Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

“Shugaban yan sandan reshen Odogbolu, Afolabi Yusuf, ya jagoranci tawagar jami’ansa zuwa wajen da abun ya faru, amma tuni wadanda ake zargin sun cire kokon kan gawar sun wuce.

“Sai yan sandan suka shiga bincike wanda ya yi sanadiyar kama ma’auratan da wasu mutum biyu.

“Su duka ukun sun fallasa cewa sune suka haka kabarin sannan suka cire kan gawar.

“Sannan daga bisani suka dauki jami’an tsaron zuwa Ikenne, inda mutum na hudu wanda ya bukaci su kawo kan don yin asiri yake, inda aka kama shi,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun sace darekta a gwamnatin jihar Zamfara tare da wasu mutane 5

Kwamishinan yan sandan jihar, Edward Ajogun, ya umurci da a gaggauta tura masu laifin zuwa ga sashin binciken miyagu domin ci gaba da bincike da hukunta su.

A wani labari na daban, wani bakaniken kan hanya dake unguwar Nkwola Eziama a jihar Imo ya gudu da motar wadanda suka bashi gyara.

Kamar yadda wani mawaki ya wallafa ranar Asabar, 26 ga watan Satumba, wata Chinyere Ezeji ta ce motarsu ta tsaya a wuraren layin Amala/Eziama ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel