ICPC ta samo N16 biliyan daga ma'aikatar gona ta tarayya

ICPC ta samo N16 biliyan daga ma'aikatar gona ta tarayya

- Hukumar ICPC ta tabbatar da cewa ta samo naira biliyan 16 daga ma'aikatar gona ta tarayya a 2020

- Farfesa Bolaji Owansaye, ya sanar da cewa sun bankado kudaden bayan sama da fadi da aka yi dasu daga ma'aikatar

- An adana su a wasu asusu masu zaman kansu yayin da aka yi amfani da damar raba tallafin korona

Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta ce ta samo naira biliyan 16 daga ma'aikatar gona ta tarayya a 2020.

Shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owansaye, ya bayyana hakan a wani taro ta yanar gizo da yayi a kan yaki da raashawa.

Owasanye ya ce, kudaden an kwashesu ne ta wata hanya abar zargi kuma aka saka wani asusu ba tare da sanin babban akantan tarayya ba.

Ya ce ma'aikatar ta janye kudin inda ta saka su a wani asusun baki wanda baya cikin na babban bankin tarayya.

Kamar yadda Owasanye yace, wasu daga cikin kudaden da aka samo an tura su asusun bankuna masu zaman kansu, yayin da wasu aka yi amfani dasu ba ta hanyar da ta dace ba.

"A yayin da ake cikin bincike a kan tsaikon da aka samu sakamakon cutar korona, babban bankin Najeriya ya saki kudaden domin ma'aikatar tace tana bukatar kudi domin rarrabe kayan tallafi.

A halin yanzu, hukumar na bibiyar \yadda aka kashe kudaden," yace.

KU KARANTA: Osinbajo ya bayyana lokacin bude iyakokin kasar nan

ICPC ta samo N16 biliyan daga ma'aikatar gona ta tarayya
ICPC ta samo N16 biliyan daga ma'aikatar gona ta tarayya. Hoto daga @Dailytrust
Source: Twitter

KU KARANTA: Sarautar Zazzau: Tsaro ya tsananta a gidan Yariman Zazzau, Mannir Jaafaru

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka mai zaman kanta (ICPC), a ranar Litinin, ta ce ta bankado makuden kudi har N2.67 biliyan na ciyar da 'yan makaranta amma a asusun bankuna masu zaman kansu.

ICPC ta ce kudin da aka waskar zuwa asusun bankuna masu zaman kansu, an bada ne domin ciyar da yara 'yan makaranta amma kuma suna gida.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana hakan yayin taron gangami a kan yaki da rashawa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel