Barakar da Najeriya ke ciki a yanzu za ta iya tarwatsa ta - Osinbajo

Barakar da Najeriya ke ciki a yanzu za ta iya tarwatsa ta - Osinbajo

- Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya ce akwai bukatar toshe barakar da ke kunno kai

- Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin shagalin cikar Najeriya shakaru 60 da samun 'yancin kai

- Ya sanar da cewa, rashin toshe barakar da ke kunno kai na iya tarwatsa kasar Najeriya matukar ba a dauka mataki ba

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai yuwuwar tarwatsewar Najeriya idan ba'ayi kokarin toshe barakar dake kunno kai ba.

Yace akwai wadanda zasu iya yunkurin hana toshe barakar, amma idan aka jajirce kuma aka dage da addu'a za'a iya cimma gaci.

Osinbajo yayi wannan jan kunnen ne a ranar Lahadi a Abuja a wata tattaunawa da aka yi da shi, saboda shiryawa shagalin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai na Najeriya.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci mataimakin shugaban kasar, The Punch ta wallafa.

Cikin mutanen da suka samu damar halarta har da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; shugaban ma'aikatan tarayya; Folshade Yemi-Esan; manyan sakatarorin gwamnati, mayakan tsaro da sauran manyan mutane.

KU KARANTA: Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta

Barakar da Najeriya ke ciki a yanzu za ta iya tarwatsa ta - Osinbajo
Barakar da Najeriya ke ciki a yanzu za ta iya tarwatsa ta - Osinbajo. Hoto daga @Thepunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai sa ran gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kasa nan kusa.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe iyakokin kasa a watan Oktoba 2019 saboda hana shigowa da kaya da makamai Najeriya, da kuma kiyaye kasuwancin cikin kasa.

Shuwagabannin kasashe kamar Ghana da jamhuriyar Benin sunyi ta rokon shugaban kasa akan ya taimaka ya bude iyakar, amma ya runtse idanunsa yace sam ba zai bude ba har sai kwamitin da ta zartar da rufewar ta duba lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel