ICPC ta bankado inda aka yi da N2.67 biliyan ta ciyar da 'yan makaranta

ICPC ta bankado inda aka yi da N2.67 biliyan ta ciyar da 'yan makaranta

- Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC), ta sanar da cewa ta bankado inda aka zuba kudaden ciyar da yara 'yan makaranta

- Hukumar ta tabbatar da cewa, ta samo makuden kudi har N2.67 biliyan daga wasu asusun bankuna masu zaman kansu

- Lamarin ciyar da 'yan makaranta a lokutan cutar korona ya janyo cece-kuce daga wurin jama'a masu tarin yawa

Hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka mai zaman kanta (ICPC), a ranar Litinin, ta ce ta bankado makuden kudi har N2.67 biliyan na ciyar da 'yan makaranta amma a asusun bankuna masu zaman kansu.

ICPC ta ce kudin da aka waskar zuwa asusun bankuna masu zaman kansu, an bada ne domin ciyar da yara 'yan makaranta amma kuma suna gida.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana hakan yayin taron gangami a kan yaki da rashawa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Farfesa Owasanoye ya ce an bankado N2.5 biliyan wanda babban ma'aikacin a ma'aikatar gona ya killace domin kansa.

Hukumar ta kara da bayyana cewa, ta samu wasu gine-gine 18, farfajiyar kasuwanci 12 da filaye 25, Vanguard ta wallafa.

Ya ce cibiyoyin gwamnati 33 ne suka yi bayani a kan N4.1 biliyan da aka tura ta TSA, N4.2 biliyan kuwa har yanzu babu bayani.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki (Hotuna)

ICPC ta bankado inda aka yi da N2.67 biliyan ta ciyar da 'yan makaranta
ICPC ta bankado inda aka yi da N2.67 biliyan ta ciyar da 'yan makaranta. Hoto daga @Thepunch
Source: UGC

KU KARANTA: Sanata Marafa ya aurar da diyarsa tare da marayu 13 a Kaduna

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai sa ran gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kasa nan kusa.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe iyakokin kasa a watan Oktoba 2019 saboda hana shigowa da kaya da makamai Najeriya, da kuma kiyaye kasuwancin cikin kasa.

Shuwagabannin kasashe kamar Ghana da jamhuriyar Benin sunyi ta rokon shugaban kasa akan ya taimaka ya bude iyakar, amma ya runtse idanunsa yace sam ba zai bude ba har sai kwamitin da ta zartar da rufewar ta duba lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel