Dakarun soji sun tsananta wa 'yan bindiga, sun ragargaza maboyarsu a Borno

Dakarun soji sun tsananta wa 'yan bindiga, sun ragargaza maboyarsu a Borno

- Hedkwatar tsaro ta kasa ta sanar da yadda rundunar Operation Lafiya Dole ta kawar da 'yan ta'adda

- Kamar yadda kakakin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche ya sanar, dakarun sun ragargajesu ta jiragen yaki

- Enenche ya ce bayanai sun tabbatar da cewa mayakan ta'addancin suna da sansani a Dikwa da ke Warshale

Hedkwatar tsaro ta ce rundunar sojojin sama ta Operation Lafiya Dole ta kawar da yan ta'adda da dama kuma ta lalata kayan aikinsu a hari jirgin sama a Arina Woje, Warshale da Valangide a Borno.

Shugaban fannin yada labaran tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya sanar da hakan ranar Litinin a Abuja.

Enenche yace, anyi harbin ne ta jirgin sama a ranar 26 ga watan Satumba, cikin kwarewa da dabara irin ta yan ISR.

Yace an gano yan ISWAP din suna zama a Arina Woje da karamar hukumar Marte, The Punch ta wallafa.

Kakakin ya ce ta jirgin sama sojojin saman suka yi ta kai harbi suna lalata maboyar yan ta'addan.

Enenche yace an gano yan ta'addan da suka kai hari Dikwa a Warshale, sakamakon ragargazar da NAF suka yi musu ta jirgin sama.

A dayan bangaren, yayi bayani akan yadda sojojin saman suka kai wa yanta'adda hari a dajin Sambisa da daddare, inda suka yiwa 'yan ta'addan kaca-kaca.

KU KARANTA: Hotunan jerin motocin alfarma 10 masu matukar tsada a duniya

Dakarun soji sun tsananta wa 'yan bindiga, suna ragargaza maboyarsu a Borno
Dakarun soji sun tsananta wa 'yan bindiga, suna ragargaza maboyarsu a Borno. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sabbin mutum 126 sun sake kamuwa da korona

A wani labari na daban, samamen da dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole karkashin Operation Hail Storm 2 suka aiwatar suke aiwatar ya cigaba da bada sakamako mai kyau.

Na karshen da ya faru shine ragargaza sansanin mayakan ta'addanci da kuma halaka wasu daga cikin 'yan Boko Haram da ke Tongule, Bone da Isari B Musa a ranar 24 ga watan Satumban 2020.

Samamen da dakarun suka kai Tongule an kai shi ne sakamakon tabbacin da suka samu na cewa 'yan ta'addan na zama a yankin da dare kadai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel