Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda ya yi batanci ga Annabi a Kano

Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda ya yi batanci ga Annabi a Kano

- Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Nigeria da ta yafewa mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW)

- Majalisar ta ce yin waka ba laifi bane, don haka, yanke hukuncin kisan ya sabawa dokar yancin dan Adam ta kasa da kasa

- Banda Yahaya Aminu Sharif, akwai kotun da ta yankewa wani dan shekaru 13 hukuncin shekaru 10 a gidan kaso, bisa zarginsa da batanci ga Annabi

A ranar Litinin, kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci Nigeria da ta saki mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A watan da ya gabata ne wata kotun shari'a a Kano, ta yankewa Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa, bayan da ya yi wakar batanci ga Musulunci da Annabi, kuma ya raba a WhatsApp.

A cikin wata sanarwar hadin guiwa daga kwararrun MDD, sun bayyana cewa "Waka ba laifi bace," kuma suka bayyana cewa tun farko mawakin bai samu kwararrun lauyoyi ba ne.

KARANTA WANNAN: APC ta yi babban rashi a jihar Delta, tsohon gwamna ya koma PDP

Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda da ya yi batanci ga Annabi a Kano
Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda da ya yi batanci ga Annabi a Kano - @bbchausa
Source: Twitter

Ita ma wata kwararra a hakkokin al'adun bil Adama, Karima Bennoune, ta bayyana cewa, sabawa dokar yancin dan Adam ne yanke hukuncin kisa don an yi waka tare da raba ta a kafofin sadarwa.

Ta roki Nigeria da ta janye wannan hukuncin kisan, kana ta tabbatar da tsaron lafiyar mawakin har zuwa lokacin da zai daukaka kara kan hukuncin.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu

Fusatattun mutane sun gudanar da zanga zanga bayan da Sherif ya yi wakar, inda suka kona gidan iyayensa a ranar 4 ga watan Maris.

Bangaren shari'a na Nigeria na ci gaba da fuskantar suka tun bayan da ta yankewa dan shekaru 13 hukuncin shekaru 10 a gidan kaso, bisa zarginsa da batanci ga Annabi a wata muhawara.

Shi ma Daraktan kula da gidan tarihin Auschwitz, Omar Farouq, ya bukaci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yafe wa yaron da ya yi batanci ga addini a Kano.

A wani labari, Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Elrufai ya musanta labarin da ake yadawa a kafafen watsa labarai na cewar ya karbi sunaye daga masu zaben sarkin Zazzau.

A cewar gwamnan, wannan labarin kanzon kurege ne kawai, kasancewar har yanzu, babu wani suna da ya zo gabansa, da sunan tantancewa don nada sabon sarki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel