Da duminsa: Sabbin mutum 126 sun sake kamuwa da korona

Da duminsa: Sabbin mutum 126 sun sake kamuwa da korona

- Hukumar kula da cuttuka masu yaduwa ta Najeriya, ta sanar da sake kamuwar sabbin mutum 126 da cutar korona

- Hakan ya bayyana a ranar 27 ga watan Satumban 2020 daga shafin hukumar na kafar sada zumunta ta Twitter

- Hukumar NCDC ta sanar da hakan wurin karfe 11 na daren ranar Lahadi

Alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC), na ranar 27 ga watan Satumban 2020 ya tabbatar da cewa sabbin mutum 126 sun sake kamuwa da cutar korona.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Asabar 27 ga Satumba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 126 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

FCT-30

Lagos-24

Rivers-23

Ogun-13

Katsina-9

Plateau-9

Ondo-6

Kaduna-4

Kwara-4

Imo-2

Bauchi-1

Edo-1

KU KARANTA: Tirkashi: Mutane sun yiwa Donald Trump ihun bama yi a lokacin da suka je jana'iza

Jimilla masu cutar - 58324

Wadanda aka sallama bayan warkewa - 49794

Wadanda suka rasu - 1108

KU KARANTA: Yadda bai wa PDP damar lallasa APC a zaben Edo - Buhari ya yi bayani

A wani labari na daban, wata mata mai dauke da juna biyu ta fada cikin ruwa don ceton rayuwar mijinta lokacin da wani katon kifi ya kai mishi farmaki a Florida.

A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba wani kifi ya kaiwa wani mutumi mai suan Andrew Eddy, mai shekaru 30 da haihuwa farmaki, yayin da yake cikin jirgin ruwansa a yankin Sombrero a Florida.

A yadda rahotonni suka nuna, katon kifin ya ciji kafadar mutumin ne, sakamakon haka ya sanya take a wajen jirgin ya kife cikin ruwa. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel