Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta

Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta

- Matashi Usman Abubakar dan asalin jihar Katsina, ya yayyaga takardun makarantarsa baki daya

- Kamar yadda kafofin sada zumunta suka bayyana tare da hoton matashin, an tabbatar da cewa ya kammala hidimtawa kasa

- Dalilinsa na yaga takardunsa dukkansu kuwa tare da banka musu wuta bai wuce fusatar da yayi saboda rashin aikin yi ba

Hotunan fusataccen matashin da ya yayyaga takardun makarantarsa dukkansu ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Kamar yadda hotunan suka karade kafofin sada zumuntar zamani na Twitter da Facebook, an ga matashin ya yaga takardunsa sannan ya banka musu wuta.

An gano cewa, matashin dan asalin jihar Katsina ya kammala karatunsa har zuwa matakin digiri amma samun aiki ya gagara.

Matashin mai suna Usman Abubakar, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya bayyana, ya kammala hidimar kasarsa.

Wasu jama'a sun alakanta halin da ya shiga da kasar nan yayin da wasu ke cewa gajen hakuri ne rashin hankali ya kai saurayin ga wannan aika-aikar.

Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta
Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki

Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta
Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki (Hotuna)

Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta
Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta
Hotunan fusataccen matashi mai digiri ya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

A wani labari na daban, a ranar Asabar Sanata Kabiru ya bada auren diyarsa Architect Aisha da wasu marayu 13 a cikin taron mutane da dama a jihar Kaduna.

Marayun guda 13 da ya aurar sun rasa iyayensu ne sakamakon ta'addancin yan bindiga a jihar Zamfara.

An daura auren a masallacin juma'ar Almannar dake GRA Unguwar Rimi, kuma limamin masallacin, Dr Tukur Adam Almannar ya daura auren.

A lokacin daurin auren, limamin ya shawarci masu matsayi a gwamnati da masu hannu da shuni da su yi koyi da Sanatan, wurin kula da marayu a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel