El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili

El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili

- Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta yi watsi da rahoton 'yan majalisar nadin sarakuna a masarautar Zazzau

- Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana zarginsu da karbar cin hanci daga daya daga cikin masu zawarcin karagar

- A halin yanzu gwamnan ya buakci dukkan masu bukatar kujerar su fito domin sabunta tantancewa daga jami'an tsaro

Gwamnatin jihar Kaduna ba za ta yi amfani da rahoton da majalisar nadin sarki na masarautar Zazzau ta kai mata ba domin cike gurbin sarkin Zazzau, wata majiya da ta san kan lamrin ta tabbatar wa da Premium Times.

Wannan hukuncin ya dawo da Ahmed Bamalli, wanda aka tabbatar da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ke so a cikin masu zawarcin karagar mulkin.

Premium Times ta gano cewa, gwamnan ya yanke wannan hukuncin bayan zargin da yayi an bai wa wasu daga cikin 'yan majalisar cin hanci.

A farkon makon nan ne aka gano cewa, 'yan gidajen sarautu hudu ne daga gidaje uku na sarautar Zazzau suka fito neman kujerar.

Sun hada da Iyan Zazzau, Bashir Aminu; Magajin Garin Zazzau, Ahmed Bamalli; Yeriman Zazzau, Munir Ja’afaru da Turakin Zazzau, Aminu Idris.

Daga cikin mutum hudun, 'yan majalisar sun mika sunayen mutane uku inda Ahmed Bamalli bai samu shiga ba.

Wata majiya daga fadar ta tabbatar da cewa, sunan Ahmed Bamalli bai shiga jerin bane saboda hatta kakansa bai yi sarautar Zazzau ba.

KU KARANTA: Boko Haram: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda a sansaninsu a Borno (Bidiyo)

El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili
El-Rufai ya yi watsi da 'yan takarar da majalisar nadin sarkin Zazzau suka bada, ya bada dalili. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

KU KARANTA: Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewa, daya daga cikin masu neman kujerar ya bai wa 'yan majalisar cin hanci kafin su mika rahoton gaban gwamnan.

Hakan ce ta sa gwamnan ya yi kira ga dukkan masu neman karagar da su dawo a sake sabuwar tantancewa.

Jimillar masu neman kujerar sun kai mutum 11 kuma an samo sabuwar hanyar tantacewa wacce jami'an tsaro ce za su yi.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, bayan gajeriyar rashin lafiya.

Sarkin ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a ranar Lahadi. "Cike da alhini nake tabbatar da mutuwar baban jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr, Shehu Idris Idris," El-Rufai ya wallafa a Facebook.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel