Sanata Marafa ya aurar da diyarsa tare da marayu 13 a Kaduna

Sanata Marafa ya aurar da diyarsa tare da marayu 13 a Kaduna

- A ranar Asabar, Sanata Kabiru ya bada auren diyarsa Architect Aisha da wasu marayu 13 a Kaduna

- Sakamakon kamarin da ta'addanci a yayi a jihar, marayun 13 suka rasa iyayensu

- An daura auren a masallacin juma'ar GRA Unguwar Rimi, kuma limamin masallacin, Dr Tukur Almannar ya daura auren

A ranar Asabar Sanata Kabiru ya bada auren diyarsa Architect Aisha da wasu marayu 13 a cikin taron mutane da dama a jihar Kaduna.

Marayun guda 13 da ya aurar sun rasa iyayensu ne sakamakon ta'addancin yan bindiga a jihar Zamfara.

An daura auren a masallacin juma'ar Almannar dake GRA Unguwar Rimi, kuma limamin masallacin, Dr Tukur Adam Almannar ya daura auren.

A lokacin daurin auren, limamin ya shawarci masu matsayi a gwamnati da masu hannu da shuni da su yi koyi da Sanatan, wurin kula da marayu a jihar.

"Angon diyar Sanatan, Al'amin Ilyasu Abdullahi, ya biya naira 100,000 a matsayin sadakin Aisha Kabiru Marafa a bisa sunnar manzon Allah(SAW).

"Sauran amaren 13 marayu ne da Sanatan ya dauki nauyin bada aurensu tare da diyarsa. Muna rokon Allah ya biyashi," in ji Limamin.

Dr Tukur ya ce, Sanatan ya yi duk abinda uba yake yiwa yaransa, akan diyarsa da marayun 13.

Ya kara da cewa, "Annabi Muhammad ya hori musulmai da kulawa da marayu tsakaninsu."

KU KARANTA: Boko Haram: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda a sansaninsu a Borno (Bidiyo)

Sanata Marafa ya aurar da diyarsa tare da marayu 13 a Kaduna
Sanata Marafa ya aurar da diyarsa tare da marayu 13 a Kaduna. Hoto daga @Dailytrust
Source: Twitter

KU KARANTA: Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno

Sanata Kabiru Marafa ya sanar da yan jarida bayan daurin auren cewa, akwai marayu da dama a Zamfara da suka yi ta yabon sanatan saboda yanmata da dama a jihar sun kai munzalin aure amma iyayensu basu da ko tsintsiya balle su aurar da su.

Ya ce yayi mamakin yawan al'ummar da suka halarci daurin auren, saboda yaso ayi auren a sirrance saboda rashin tsaron da ke jihar Zamfara.

Akwai manyan mutane da dama da suka samu damar halartar daurin auren kamar: Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle; tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmuda Shinkafi; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi, tare da sanatoci da manyan masu mulki dake kasar nan.

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta ce tana sake matsanta wa Darul-Salam domin tabbatar da cewa duk wata barazana daga kungiyar ta kaura, Daily Trust ta tabbatar.

Shugaban fannin yada labarai na tsaro, Manjo janar John Enenche, ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyi daga manema labarai yayin zantawar mako-mako a kan ayyukan rundunar a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel