Sultan Hassanal Bolkiah: Hamshakin mai arzikin da ya mallaki Rolls Royce 500, N7m kudin askinsa

Sultan Hassanal Bolkiah: Hamshakin mai arzikin da ya mallaki Rolls Royce 500, N7m kudin askinsa

- Sultan din Brunei, Hassanal Bolkiah, wanda dukiyarsa ta kai $40 biliyan (N15,500,000,000,000), ya mallaki motoci kirar Rolls-Royce 500 kuma ya kafa tarihi a duniya

- Basaraken ya gina fada mai dakuna 1,788, wacce Architect Leandro Locsin ya zana kuma hakan ya zama babban tarihi

- An gano cewa, Bolkiah yana kashe $20,000 (N7,750,000) a kowanne askin gashinsa da ake masa daga cikin facakar da yake da dukiyarsa

Sarkin Brunei, Hassanal Bolkiah, ya kasance daya daga cikin sarakunan duniya masu tarin dukiya.

Kamar yadda Insider ta wallafa, ya taba mallakar dukiyar da ta kai $40 billion (N15,500,000,000,000) a duniya.

Wasu daga cikin yanayin facakar da yake da kudinsa sun hada da tseren motocin kirar Ferrari a cikin dare a babban birnin Brunei, gina gida mai dakuna 1,788 da kuma kashe $20,000 (N7,750,000) domin aski.

Basaraken ya gaji mahaifinsa mai suna Sultan Omar Ali Saifudeen, wanda ke da 'ya'ya 10 da mata da yawa.

Mahaifin Bolkiah ya sauka daga karagar mulki a 1967 kuma ya nada shi sarki a lokacin da yake makarantar horar da hafsin soja ta Ingila.

Bolkiah ya hau karagar mulin bayan ya kammala karatunsa. An gano cewa, ana kiransa da 'Playboy' sakamakon shagali da mata da yayi fice a kai.

Babbar fadarsa ta kai kafa 2.2 miliyan a fadi. Babban magini Leandro Locsin ne ya ginata. Ta shiga littafin tarihin duniya a matsayin fadar da ta fi kowacce girma a duniya.

Wani abun mamaki shine yadda ahalinsu basaraken suka siya rabin motoci kirar Rolls Royce a duniya baya ga wasu motocin alfarma da suka mallaka.

KU KARANTA: Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno

Sultan Hassanal Bolkiah: Hamshakin mai arzikin da ya mallaki Rolls Royce 500, N7m kudin askinsa
Sultan Hassanal Bolkiah: Hamshakin mai arzikin da ya mallaki Rolls Royce 500, N7m kudin askinsa. Hoto daga Camudi
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, Marigayi Alhaji Mai Deribe babu shakka yana daya daga cikin hamshakan masu kudi a Najeriya a shekarun 1980. Ya gina gida wanda aka yi shi da ruwan zinari sannan ya mallaki wani jirgin sama kirar Gulfstream G550.

Kamar yadda Northeast Reporters suka wallafa, yana daya daga cikin mutane 12 da suka taba mallakar irin wannan jirgin saman a fadin duniya.

Gidansa, wanda ake kira da Gidan Deribe, ya ja hankulan jama'a masu tarin yawa a duniya. Ba abun mamaki bane ganin yadda ya dinga saukar manyan mutane a duniya kamar Yarima Charles da matarsa, marigayiya Gimbiya Diana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng