Buhari ya jajantawa Zulum bisa harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa a Borno

Buhari ya jajantawa Zulum bisa harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa a Borno

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagar Gwamna Zulum a ranar Juma'a a Borno inda suka kashe jami'an tsaro da na JTF

- Shugaban kasar ya ce wannan harin wani yunkurin ne da 'yan ta'addan ke neman yi don hana mayar da 'yan gudun hijiran gidajensu

- Ya kuma yaba wa jarumtar jami'an tsaron da tare da yin addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya bawa iyalansu hakurin jure rashi

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya yi Allah wadai ta harin da aka kai wa tawagar gwamnan Borno, Babagana Zulum da ya yi sanadin rasuwar jami'an tsaro da wasu 'yan civilian JTF.

An tabbatar da mutuwar a kalla jami'an tsaro 11 a harin na ranar Juma'a, wanda shine na biyu da ake kai wa tawagar Zulum a jiharsa.

Buhari ya jajantawa Zulum bisa harin da 'yan ta'adda suka ka wa tawagarsa
Buhari ya jajantawa Zulum bisa harin da 'yan ta'adda suka ka wa tawagarsa. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zan mara wa Tinubu idan ya fito takarar shugaban kasa - Buhari

A sanarwar da ta fito daga kakakin shugaban kasa Garba Shehu, shugaban kasar ya ce harin a aka kai a hanyar Maiduguri - Baga wani mataki ne na hana mayar da 'yan gudun hijira gidajensu.

"Cikin alhini bisa rasa rayyukan da aka yi a tawagar gabannin mayar da 'yan gudun hijirar gidajensu, Buhari ya yi wa iyalai da masoyansu jaje," a cewar sanarwar ta Shehu.

"Shugaban kasar ya shawarci gwamnatin Borno da ke aiki tare da hukumomin tsaro da tattara bayannan sirri da kada su karaya game da aikin da suka sa a gaba na ceto garuruwan daga 'yan ta'addan Boko Haram."

KU KARANTA: Bidiyo: Harin da sojoji suka kai wa 'yan Boko Haram a Bula Sabo da Dole a Borno

A cewar sanarwar, Shugaban kasar ya kuma bukaci hukumomin tsaro da na tattara bayannan sirri su kara kwazo wurin samar da tsaro a hanyoyin da ke jihar.

"Shugaban kasar ya yabawa jarumtar jami'an tsaron da suka fafata da 'yan ta'addan da kuma kokarin Gwamna Zulum da ke aiki tare da sojoji domin kawo karshen 'yan ta'addan, sake gidan gidaje ya kuma mayar da 'yan gudun hijira gidajensu," a cewar sanarwar.

"Ya yi addu'ar Allah ya jikan jami'an tsaro da 'yan sa kai na JTF da suka rasu ya bawa iyalansu hakurin rashi."

A wani rahoton daban, kun ji Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel