Shin da gaske ne kungiyar malaman jami'a ASUU sun janye daga yajin aiki?

Shin da gaske ne kungiyar malaman jami'a ASUU sun janye daga yajin aiki?

- Shin meyasa ake yada labaran da basu da tushe?

- Ko dai dalibai sun kosa su koma makaranta ne bayan watanni bakwai a gida?

- Kungiyar ASUU ta magantu kan lamarin janyewa daga yajin aiki

Kungiyar Malaman jami'o'i a Najeriya ta yi watsi da jita-jitan da ke yawo a kafofin ra'ayi da sada zumunta cewa mambobinta sun janye daga yajin aikin da suka tafi tun watan Maris.

Kungiyar ta yi tsokacin haka ne ta shafinta na Tuwita yayinda matasa a Tuwita suke gaddama kan janye yajin aikin.

A cewar kungiyar, rahoton karya ne, na bogi ne, kuma babu kamshin gaskiya ciki.

"Sabanin rade-radin dake yawo a kafafen ra'ayi da sada zumunta cewa kungiyar Malaman jami'a ASSU sun janye yajin aikin, babu gaskiya cikin haka."

"Idan zamu janye yajin aiki, akwai matakai da ake bi kuma har yanzu bamu bi matakan ba." Kungiyar tace.

Shin da gaske ne kungiyar malaman jami'a ASUU sun janye daga yajin aiki?
Credit: @asuu
Source: Twitter

KU KARANTA: Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemu, ya lashi takobin cewa kungiyar ba zata gushe tana yaji ba har sai gwamnatin tarayya ta biya dukkan bukatunta.

Ogunyemi ya ce ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar 2012 da akayi..

Ya kara da cewa abin takaici ne ace tun shekarar 2009 malaman jami'a basu samu sauyin albashi ba. Ya jaddada cewa wajibi ne a duba lamarin kafin ASUU ta janye wannan yajin aikin.

A cewarsa, "Ga matsalan albashi; ba'a magance ba. Da alamun akwai wasu kusoshi a gwamnati da suka rantse sai mambobinmu sun wahala ta hanyar rike musu albashi."

Malaman Jami'a sun shiga yajin aiki gab da bulluwar cutar Korona a wata Maris.

Tun daga lokacin daliban jami'o'in gwamnati dake kasar gaba daya suke zaune a gida.

KU DUBA: Minista Sadiya ta auri babban hafsan mayakan Sojin sama, Sadiq Baba

A bangare guda, Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyoyin sufurin jiragen sama guda hudu, za su bi sahun kungiyar kwadago ta kasa NLC, shiga yajin aiki a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, kungiyoyin sun bukaci ma'aikatansu a sufurin jiragen sama da su yi zamansu a gida daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel