Gurfanar Obasanjo a gaban tsoho mai shekaru 94 ya janyo cece-kuce

Gurfanar Obasanjo a gaban tsoho mai shekaru 94 ya janyo cece-kuce

- Hoton tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya jawo cece-kuce a lokacin da aka ganshi yana nuna matukar girmamawa ga Pa Reuben Fasoranti a Akure

- Mai daukar hoto ya dauki hoton daidai lokacin da Obasanjo ya gurfana a gaban tsohon, lokacin da yakai mishi ziyara

- Pa yana zaune a kan kujera yana murmushi, yayin da tsohon shugaban kasar yake zaune a kasa sanye da kayansa na gargajiya

Wani hoto ya bayyana wanda ya nuna tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Akure, jihar Ondo, da Pa Reuben Fasoranti, wanda shekarar haihuwarsa bata dade da zagayowa ba.

Ba hoton ne abin bada labari ba, abin da tsohon shugaban kasar yayi a cikin hoton shine yafi zama abin bada labari.

Don girmama tsohon mai shekaru 94 da haihuwa, Pa Reuben Fasoranti, dattijon da Obasanjo ya kaiwa ziyara, tsohon shugaban kasar ya zauna a kasa.

Hakika, halin Obasanjo na ba wa manya girma, abin yabo ne da burgewa. Sannan duk inda yake, sai ya nishadantar da mutane.

A wani hoto da jaridar PM News suka wallafa, tsohon shugaban kasar yana zaune a kasa, yana murmushi da hularsa ta Yarabawa a kansa.

Kamar yadda aka dauki hoton tsohon mai shekaru 94 da haihuwa yana zaune akan kujera. Obasanjo na zaune kasa tare da Basorun Seinde Arogbofa.

KU KARANTA: Kyakyawar budurwa ta sha kunya, ta ce tana son saurayi amma yace ta cigaba da nema

Gurfanar Obasanjo a gaban tsoho mai shekaru 94 ya janyo cece-kuce
Gurfanar Obasanjo a gaban tsoho mai shekaru 94 ya janyo cece-kuce. Hoto daga PM News
Source: UGC

KU KARANTA: Dirarriyar budurwa ta wallafa hotunanta, ta bukaci duk saurayin da ke da bukata ya nemi soyayyarta

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba, ya ce ya dauka alhakin lallasa APC da aka yi a zaben ranar Asabar da ta gabata na gwamnoni.

Shugaban kasar ya sanar da hakan a gidan gwamnati bayan karbar sabon gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki, tare da mataimakinsa Philip Shaibu da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP.

Buhari ya ce a matsayinsa na babban jiigo a jam'iyyarsa, shine yakamata a dora wa laifin komai ballantan a lokacin da aka lallasa su a zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel