Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya Pete Edochie martani

Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya Pete Edochie martani

- Kungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN da aka fi sani da Shi'a a Najeriya ta ce ba su ji dadin irin yadda jarumi Pete Edochie ya yi a wani fim da ake shirin fitarwa ba

- Shugaban sashin watsa labarai na kungiyar, Ibrahim Musa ya ce duk da hakan ba gaskiya bane sunyi barazana ga rayuwarsa domin su masu son zaman lafiya ne

- Musa ya yi ikirarin cewa Shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanat Tukur Buratai ne ya dauki nauyin fim din da nufin nuna kamar kungiyar ta masu son tayar da fitina ne

Shugaban sashin watsa labarai na kungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN, Ibrahim Musa ya nesanta kungiyar da barazanar kisar da jarumi Pete Edochie ya ce ana masa saboda fitowa a fim din 'Fatal Arrogance' a matsayin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya kwaikwayi Zakzaky martani
Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya kwaikwayi Zakzaky martani. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zan mara wa Tinubu idan ya fito takarar shugaban kasa - Sanata Buhari

A hirar da Musa ya yi da Alexander Okere wadda The Punch ta ruwaito ya ce kungiyar bata taba yi wa kowa barazana ba tsawon shekaru 40 da kafuwarsu a Najeriya sai dai sune ake kai wa hari.

Ya cigaba da cewa ba su gamsu da dalilan da jarumin ya bayar ba na cewa shi aikinsa kawai ya yi a matsayin jarumi amma ba shi ya rubuta fim din ba, "A matsayinsa na kwararren jarumi ya kamata ya karanta labarin ya kuma san dalilin yinsa."

Har wa yau, ya ce ya ikirarin cewa kowa ya lura da irin tufafin da Edoche ya saka a fim din ya san Sheikh Zakzaky ake kwaikwayo.

KU KARANTA: Fitattun sarakunan arewa 7 da rasuwarsu ya girgiza mutanen Najeriya a 2020

Sannan ya yi ikirarin cewa Shugaban hafsin sojojin kasar Najeriya Laftanar Tukur Buratai ne ya dauki nauyin shirya fim domin sauya abinda ya faru tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a nuna kamar su mutane ne masu son tayar da fitina.

"Ka duba irin tufafin da suka saka kuma suna zanga-zanga suna ambaton ‘Allahu akbar. La ilaha illallah.’ Haka muke zanga-zanga kamar yadda aka sani."

Da aka masa tambaya ko yana da hujjar cewa Buratai ne ya dauki nauyin yin fim din, ya ce, "Mun san wanda ya rubuta littafin 'Fatal Attraction' ka duba yadda ya yi kama da 'Fatal Arrogance' kuma dama marubucin mai yi wa sojoji kwangila ne duk cewa suna buya karkashin kungiyoyin jin kai."

Musa ya ce kungiyar ta nemi kada a fitar da fim din duba da cewa an bata musu suna cikin fim din kuma idan aka fitar za su garzaya kotu su bi hakinsu.

A wani rahoton, an kashe jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, a daren ranar Laraba yayin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da dilalan bindiga a kauyen Kalong da ke karamar hukumar Shendam ta jihar Plateau.

Daily Trust ta ruwaito cewa sunan jami'in da aka kashe Barista Mukhtar Moddibo dan asalin karamar hukumar Misau daga jihar Bauchi. Read more:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel