Yajin aiki: Tilas ku zo aiki ranar Litinin - FG ga ma'aikata

Yajin aiki: Tilas ku zo aiki ranar Litinin - FG ga ma'aikata

- Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan ta suyi watsi da yajin aikin da kungiyar kwadago ta sanar su zo aiki ranar Litinin

- Kungiyar kwadagon ta yanke shawarar fara yajin aikin ne domin karin kudin man fetur da lantarki da gwamnati ta yi

- Sanarwar da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Yemi-Esan ta fitar ya ce dukkan ma'aiakata daga mataki na 12 zuwa sama su zo aiki ranar Litinin

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gargadi dukkan ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa sama da wadanda ke muhimman ayyuka su tabbatar sun zo aiki duk da yajin aikin da kungiyar kwadago ta sanar da fara yi a ranar Litinin.

Saboda annobar cutar korona, an shawarci wasu ma'aikatan gwamnatin su rika aiki daga gidajensu.

Yakin aiki: Dole ku zo aiki ranar Litinin - Gwamnatin Tarayya ta gargadi ma'aikata
Yakin aiki: Dole ku zo aiki ranar Litinin - Gwamnatin Tarayya ta gargadi ma'aikata. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Mayakan ISWAP sun afka wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno

Kungiyoyin kwadago sun sanar da cewa za su fara yajin aikin ranar Litini a kan karin kudin lantarki da na man fetur.

Sai dai shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Folashade Yemi-Esan cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da kwanan watar 25 ga watan Satumban 2020 ta umurci ma'aikata dake zuwa aiki suyi watsi da batun yajin aikin.

KU KARANTA: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

Wani sashi na sanarwar ya ce, "Bayan kirar da kungiyar kwadaga tayi na fara yajin aiki daga ranar Litinin 28 ga watan Satumban 2020, ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya tana sanar da dukkan ma'aikatan ta cewa gwamnatin tarayya na tattaunawa da kungiyar kwadagon a halin yanzu da nufin warware matsalolin tare da dakatar da yajin aikin da aka yi shirin yi."

Kazalika, gwamnatin tarayyar ta janyo hankalin ma'aikatan game da umurnin da kotun ma'aikata na kasa ta bayar na hana kungiyoyin kwadagon zuwa yajin aikin.

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ekiti ta dakatar da Babafemi Ojudu, mashawarci na musamman na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin siyasa 'saboda saba dokokin' jam'iyya.

A cikin sanarwar da jam'iyyar ta fitar, sakataren watsa labarai, Ade Ajayi ya ce tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Omotune Ojo yana cikin wadanda aka dakatar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel