Da duminsa: Sabbin mutane 213 sun kamu cutar Coronavirus yau

Da duminsa: Sabbin mutane 213 sun kamu cutar Coronavirus yau

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 213 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Juma’a 25 ga Satumba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 176 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-51

Plateau-51

FCT-29

Rivers-18

Ondo-12

Oyo-9

Osun-8

Gombe-7

Ogun-7

Kaduna-5

Enugu-4

Edo-3

Jigawa-3

Kano-3

Benue-1

Delta-1

Sokoto-1

Jimillan wadanda suka kamu: 58,062

Jimillan wadanda aka sallama: 49,606

Adadin wadanda suka yi wafati: 1,103

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta karbi kyautar rumfar gwajin cutar Korona na zamani guda uku daga hannun gwamnatin kasar Koriya.

Kasar Koriya ta baiwa Najeriya kyautan rumfunan ne ranar Alhamis a Abuja domin kasar ta kara karfin karban samfuri da yiwa mutane gwajin cutar.

Dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, Chikwe Ihekweazu, yayin karban kayayyakin ya ce lallai rumfunan zasu taimakawa Najeriya wajen kara yawan gwajin cutar.

Diraktan harkokin wajen kasar Koriya, Woochan Chang ya yabawa gwamnatin Najeriya bisa kokarinta wajen dakile annobar.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel