COVID-19: Cutar Coronavirus ta yi gangancin kama ni inji Ibrahimovich

COVID-19: Cutar Coronavirus ta yi gangancin kama ni inji Ibrahimovich

- ‘Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovich ya kamu da cutar Coronavirus

- Kungiyar Italiyar ta bada wannan sanarwa a ranar 24 ga watan Satumba

- Zlatan Ibrahimovich ya ce kwayar cutar ba ta yi dabara ba, da ta harbe shi

An tabbatar da cewa ‘Dan wasan kungiyar kwallon AC Milan Zlatan Ibrahimovich ya na dauke da kwayar cutar murar COVID-19.

AC Milan ta bayyana cewa ta sanar da hukumar da ke da alhaki game da halin da ‘dan wasan kwallon kafan ya ke ciki a yanzu.

Kamar yadda kungiyar ta Seria A ta sanar a jiya, Zlatan Ibrahimovich mai shekaru 39 a Duniya zai fara killace kansa a cikin gida.

KU KARANTA: 'Dan wasan Najeriya ya mutu a filin kwallo

Wannan sanarwa ta fito ne a daidai lokacin da ‘yan wasan AC Milan su ke shirin buga wasan sharer fage zuwa karamin gasan Turai.

Milan za ta fuskanci kungiyar Bodo/Glimt na kasar Norwegiya, idan har ta yi nasara za ta samu zuwa gasar Europa League na 2020.

Shi ma ‘dan wasan gaban na kasar Siwidin, ya tabbatar da wannan lamari, ya ce ya kamu da wannan cuta ta numfashin mashako.

Zlatan Ibrahimovich ya sanar da hakan ne a shafinsa na Tuwita, ya ce amma har a jiya wata Alhamis, babu alamun wannan cuta a jikinsa.

KU KARANTA: Tsohuwar zuma: Bale ya rabu da Real Madrid, ya koma Landan

COVID-19: Cutar Coronavirus ta yi gangancin kama ni inji Ibrahimovich
Ibrahimovich ya na dauke da kwayar ciwon COVID-19 Hoto: BBC/CNBC
Source: UGC

“A jiya (Laraba) gwaji ya nuna ba na dauke da kwayar cutar COVID-19, sai kuma yau aka ce na kamu.” Inji Zlatan Ibrahimovich a Tuwita.

‘Dan wasan ya ce: “Babu wata alamar komai ko makamancin haka. Har COVID-19 ta yi karfin da za ta kalubalance ni. Ba ta yi dabara ba.”

Idan za ku tuna fitaccen ‘dan wasan ya taba bugawa kungiyar Manchester United, Ibrahimovich ya zo Ingila ne bayan ya bar kungiyar PSG.

A 2020 Zlatan Ibrahimovich ya dawo Italiya har ya zura kwallaye biyu a wasansu da Sassuolo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel