Da duminsa: Za a rufe tasoshin jiragen sama ranar Litinin, za su shiga yajin aiki

Da duminsa: Za a rufe tasoshin jiragen sama ranar Litinin, za su shiga yajin aiki

Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyoyin sufurin jiragen sama guda hudu, za su bi sahun kungiyar kwadago ta kasa NLC, shiga yajin aiki a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, kungiyoyin sun bukaci ma'aikatansu a sufurin jiragen sama da su yi zamansu a gida daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

KARANTA WANNAN: Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari

Hakan na nufin cewa, za a rufe tashoshin jiragen sama a ranar Litinin.

"Kamar yadda kuka sani, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun sanar da matakinsu na shiga yajin aikin kasa da kasa daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba 2020," a cewar sanarwar.

"Kungiyoyinmu na ma'aikatan sufurin jiragen sama, kamar yadda aka ambaci sunayensu a sama, suna goyon bayan shiga wannan yajin aikin.

Da duminsa: Za a rufe tasoshin jiragen sama ranar Monday, za su shiga yajin aiki
Da duminsa: Za a rufe tasoshin jiragen sama ranar Monday, za su shiga yajin aiki - The Cable
Source: Twitter

"Don haka, muke kira ga dukkanin mambobinmu, da su yi zaman su a gida, ba zamu fita aiki ba, daga karfe 12 na safiyar ranar Litinin 28 ga watan Satumba, har sai idan NLC ko TUC sun fadi akasin hakan.

"Ya zama wajibi ma'aikata su bi wannan umurni."

Kungiyoyin kwadago, da suka hada da NLC da TUC, sun sha alwashin jiga yajin aiki, sakamakon karin kudin man fetur da lantarki a Nigeria.

Kafin daukar wannan mataki, kungiyoyin kwadagon sun roki gwamnati da ta janye karin kudaden da ta yi, rokon da gwamnatin ba ta amsa ba

A wani labarin, Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da cewa za ta bude makarantun Sakandire daga ranar 12 ga watan Oktoba mai kamawa.

Kwamishinan ilimi a jihar Bauchi, Dakta Aliyu Tilde, ne ya sanar da hakan ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba.

Ya ce sun amince da bude makarantun ne bayan kammala wani taro na kwamishinonin ilimi daga jihohin arewa 19 wanda aka yi a Abuja.

Yayin taron, an amince cewa jihohi za su bude makarantun sakandire kafin zuwa ranar 30 ga watan Oktoba.

Dakta Tilde ya kara da cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da ranar bude makarantun tun ranar 23 ga watan Satumba.

"Ana bukatar dukkan malamai da sauran ma su taimaka musu a makarantu su koma bakin aiki daga ranar 3 ga watan Oktoba domin fara shirye-shiryen dawowar dalibai kamar yadda gwamnati ta amince," a cewar Dakta Tilde.

Kwamishinan ya kara da cewa umarnin bude makarantun bai shafi manyan makarantun gaba da sakandire ba saboda suna da tsarinsu daban.

Bayan kara wa'adin sassauta dokar kulle a fadin Najeriya, gwamnatin tarayya ta bawa jihohi izinin bude makarantun sakandire bisa biyayya ga tsari da shawarwarin ma'aikatar lafiya da hukumar NCDC.

Jihohi da dama, musamman a kudancin Najeriya, sun sanar da ranakun bude makarantunsu na sakandire bayan samun izinin gwamnatin tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel