Yanzu-yanzu: Bangaren Shari'a ta shiga yajin aikin da NLC ke shirin yi

Yanzu-yanzu: Bangaren Shari'a ta shiga yajin aikin da NLC ke shirin yi

- Ma'aikatan bangaren shari'a a Najeriya sun ce za su shiga yajin aikin da kungiyoyin kwadago na kasar za su fara a ranar Litinin

- Kungiyoyin kwadagon sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan gwamnatin tarayya ta ki janye karin kudin man fetur da lantarki da aka yi a kasar

- Ana san ran fara yajin aikin ne a ranar Litinin 28 ga watan Satumban shekarar 2020 don tursasa gwamnati ta janye karin da NLC ta ce tsawallawa yan kasa ne

Ma'aikatan Shari'a karkashin Kungiyar Ma'aikatan Shari'a ta Najeriya, JUSUN, sun ce za su rufe kotunna a dukkan sassan kasar a ranar Litinin don biyaya ga umurnin gamayar kungiyoyin Kwadago na kasa na fara yajin aiki.

DUBA WANNAN: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

Yanzu-yanzu: Bangaren Shari'a ta shiga yajin aikin da NLC ke shirin yi
Yanzu-yanzu: Bangaren Shari'a ta shiga yajin aikin da NLC ke shirin yi. Hoto daga @SaharaReporters
Source: Twitter

Kungiyar Kwadago ta NLC da na masu sana'o'i, TUC, sun sanar da cewa za su shiga yajin aikin muddin gwamnatin tarayya ba ta janye karin kudin wutar lantarki da na man fetur da ta yi ba.

Shugaban JUSUN, Marwan Adamu, ya shaidawa The Punch a ranar Juma'a cewa a matsayinsu na wani sashi na NLC, ma'aikatan shari'a za su bi umurnin uwar kungiyar na fara yajin aikin daga ranar Litinin.

KU KARANTA: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

"Wannan yajin aikin ba na JUSUN bane, na NLC ne. A matsayin mu na mambobi a karkashin NLC dole mu yi biyayya ga umurnin zuwa yajin aikin. Saboda haka za mu shiga yajin aikin," in ji Adamu.

Da aka masa tambaya ko umurnin da Kotun Ma'aikata da ke Abuja ta bayar na dakatar da yajin aikin bai shafe su bane, Adamu ya ce, "Ba a aike mana da umurnin kotun ba, saboda haka za mu yi yajin aikin."

Adamu ya tabbatar cewa an aike da sanarwar a kotuna da ma'aikatun shari'a da dama a kasar.

A wani labarin, Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel