Yanzu-yanzu: Masu zaben sarki sun aikewa gwamna El-Rufa'i sunayen mutane 3 (Kalli makin da kowanni ya samu)

Yanzu-yanzu: Masu zaben sarki sun aikewa gwamna El-Rufa'i sunayen mutane 3 (Kalli makin da kowanni ya samu)

- Rahotanni masi siqa sun bayyana cewa ana ganawa yanzu haka a gidan gwamnatin jihar Kaduna

- Gwamna El-Rufa'i ya ce a jira sanarwarsa, kada a yada jita-jita

Masu zaben sarki a masarautar Zazzau sun gabatar da sunayen mutane uku ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i domin zaban daya cikinsu matsayin sabon sarkin Zazzau, Daily Trust ta ruwaito.

Ga sunayensu:

Alhaji Bashir Aminu, Iyan Zazzau Ya samu maki 89,

Alhaji Muhammed Munnir Jafaru, Yariman Zazzau, ya samu maki 87, da

Alhaji Aminu Shehu Idris, Turakin Karamin Zazzau ya samu maki 53 .

Yanzu haka masu zaben sarkin suna ganawa da gwamna El-Rufa'i a gidan Sir Kashin Ibrahim.

Daily Trust ta tattaro cewa Yarimomi 11 suka bayyana niyyarsu na danewa kujerar sarautar kasar bayan rasuwar tsohon sarki, Alhaji Shehu Idris ranar Lahadi.

Yanzu-yanzu: Masu zaben sarki sun aikewa gwamna El-Rufa'i sunayen mutane 3 (Kalli makin da kowanni ya samu)
Credit: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA NAN: Sabon Sarki zai fito ne daga Nahiyar Asiya inji Sanata Shehu Sani

Ba kowa zai iya neman kujeran Sarki ba

Ba dukkan yan gidan sarauta ke iya takaran kujeran sarki ba, wadanda iyayensu ko kakkaninsu suka taba sarki ne za'a iya nadawa.

Mun kawo muku rahoton cewa yarimomi daga gidajen sarauta uku cikin hudu sun bayyana niyyarsu na zama Sarkin Zazzau na 19.

Gidan sarautar Katsinawa, inda marigayin ya fito, sun gabatar da sunayen mutane hudu, na karshen shine Wamban Zazzau, Alhaji Abdulkareem Aminu.

Sauran a cewar majiyar sune, Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu; Dangaladiman Zazzau, Alhaji Aminu Idris da Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris.

DUBA NAN: Hasken Fadan Kano ya na sa rai Ahmad Bamalli ya gaji Sarki Shehu Idris

Daga gidan Mallawa, Daily Trust ta ruwaito cewa mutane uku aka gabatar, sun hada da Ciroman Zazzau, Alhaji Sa’idu Mailafiya; Barden Kudun Zazzau, Alhaji Hassan Tijjani, da Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli.

A gidan Bare-bari kuwa, mutum daya kacal aka shigar, Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel