Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

- Zababen gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa Philip Shuaibu sun kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a Abuja

- Wannan itace ziyara ta farko da Gwamna Obaseki ya kai wa shugaban kasar tun bayan zarcewarsa kan mulki karo na biyu

- Gwamna Obaseki da mataimakinsa da wasu 'yan majalisar tarayya da iyalansu sun ce sun kai ziyarar ne don yi wa shugaban kasar godiya

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan shine ziyara ta farko da Obaseki ya kai wa Buhari bayan lashe zaben gwamna karo na biyu a jihar Edo a ranar Asabar da ta gabata.

Obaseki ya lashe zabensa na farko ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, amma daga bisani ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, inda ya sake lashe zaben karo na biyu.

DUBA WANNAN: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Mataimakinsa, Mista Philip Shuaibu ya raka Obaseki zuwa fadar shugaban kasar.

Wasu daga cikin 'yan majalisa da iyalan Obaseki da Philip suma sun musu rakiya a ziyarar da suka ce sun kai wa shugaban kasar don yi masa godiya.

Ga hotunan ziyarar a kasa:

Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock
Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock. Hoto daga Aso Rock Villa
Source: Twitter

Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock
Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock. Hoto daga Aso Rock Villa
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Borno Babagana Zulum ya lashe kyautar gwarzon shugaba ta Zik

Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock
Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock. Hoto daga Aso Rock Villa
Source: Twitter

Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock
Hotuna: Gwamna Obaseki ya kai wa Buhari a Aso Rock. Hoto daga Aso Rock Villa
Source: Facebook

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ekiti ta dakatar da Babafemi Ojudu, mashawarci na musamman na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin siyasa 'saboda saba dokokin' jam'iyya.

A cikin sanarwar da jam'iyyar ta fitar, sakataren watsa labarai, Ade Ajayi ya ce tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Omotune Ojo yana cikin wadanda aka dakatar.

Ojo surukin Bola Tinubu ne, jagora na kasa na jam'iyyar ta APC mai mulki.

Ajayi ya ce an dakatar da mambobin jam'iyyar ne saboda kin janye karar da suka kai jam'iyyar a kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel