Zazzau: Mutane 8 sun gabatar da sunayensu ga masu zaben sarki

Zazzau: Mutane 8 sun gabatar da sunayensu ga masu zaben sarki

- Masu zaben sarki a masarautar Zazzau sun rufe daman gabatar da suna ga duk masu son hawa kujeran sarki

- Kawo jiya Alhamis, mutane takwas suka gabatar da sunayensu daga gidajen Sarauta uku

- Babu sunan wanda aka gabatar daga gidan sarautar Sullubawa

Yarimomin masarautar Zazzau takwas sun aikewa masu zaben sarki wasikar niyyar son gadan kujerar marigayi, Alhaji Dr Shehu Idris, Daily Trust ta ruwaito.

Bayanan da aka tattaro a daren Alhamis sun nuna cewa zuwa daidai misalin karfe 5 na yamma da kwamitin masu zaben sarki suka baiwa duka masu son zama sarki su gabatar da sunayensu, sunaye bakwai aka shigar.

Daga baya, daya daga cikin Yarimomin ya nuna rashin amincewarsa cewa ba'a sanar da shi kan wa'adin ba kuma saboda haka ya shigar da nasa wasikar da safiyar AlhamiS.

Sharadin da majalisar masu zaben sarkin suka sanya shine "idan wata gidan sarautar ta gaza amincewa kan mutum daya, kada ta gabatar da mutane fiye da uku."

Majiyar ta kara da cewa: "Saboda haka, Yarimomi daga gidajen sarauta uku, cikin, hudu, sun bayyana niyyarsu na zama Sarkin Zazzau na 19."

"Gidan sarautar Katsinawa, inda marigayin ya fito, sun gabatar da sunayen mutane hudu, na karshen shine Wamban Zazzau, Alhaji Abdulkareem Aminu."

Sauran a cewar majiyar sune, Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu; Dangaladiman Zazzau, Alhaji Aminu Idris da Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris.

Daga gidan Mallawa, Daily Trust ta ruwaito cewa mutane uku aka gabatar, sun hada da Ciroman Zazzau, Alhaji Sa’idu Mailafiya; Barden Kudun Zazzau, Alhaji Hassan Tijjani, da Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli.

A gidan Bare-bari kuwa, mutum daya kacal aka shigar, Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru.

KU DUBA: Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta dakatad da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi

Zazzau: Mutane 8 sun gabatar da sunayensu ga masu zaben sarki
Credit: @elrufai
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana wani abin birgewa da yakeyi domin wayar da kasan kafin yiwa masarautar Zazzau zaben sabon sarki bayan rasuwar marigayi Shehu Idris.

Da yammacin Alhamis, gwamna El-Rufa'i ya daura hoton wani littafin tarihi da aka wallafa kan masarautar Zazzau da yadda aka zabi sarakuna a baya.

Littafin wanda bature, M.G Smith, ya wallafa mai suna 'Government in Zazzau' na dauke da yadda salon mulkin masarautar tsakanin shekarar 1800-1950.

El-Rufa'i ya ce yana sake karanta littafin ne domin kara ilimi kafin ya yanke shawara kan wanda zai zaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel