Kungiya ta raba wa mutane 317 zakka ta N70m a Legas

Kungiya ta raba wa mutane 317 zakka ta N70m a Legas

- Kungiyar musulunci ta Lekki Muslim Ummah a Legas ta yi wa mutane 317 rabon kaya da kudi a matsayin zakka

- An raba wa mutane kudi da kuma kayayyakin sana'a da suka hada da baburan adaidaita sahu, kekunan dinki, firinji mai kankara, janareta, kwamfuta da sauransu

- Shugaban kungiyar Kamoru Omotsoho ya yi kira ga masu hannu da shuni su rika tallafawa al'umma domin ta hakan ne za su iya jin dadin arzikinsu

Kungiya ta raba wa mutane zaka na N70m a Legas
Kungiya ta raba wa mutane zaka na N70m a Legas. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za mu kafa kasar Yarabawa ba tare da tada fitina ba - Farfesa Akintoye

Wata kungiya mai suna Lekki Muslim Ummah (LEMU) a jihar Legas ta raba wa mutane 317 kudade da kayayyaki da kudinsu ya kai Naira miliyan 70 a matsayin zakka.

An kafa rukunin mutanen da suka amfana da zakka zuwa gida biyar da suka hada da wadanda aka bawa tallafin ilimi, rage talauci, kudin gidajen haya, kudin magani/asibiti da masu son biyan bashi da tallafin korona.

Kayayyakin da aka raba musu sun hada da; Adaidaita sahu 10, Kekunan dinki 17, Firinji mai kankara 28, Janareta hudu, Kwamfuta Laptop uku da babur din rabar da kaya guda daya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Shugaban kwamitin zakka na kungiyar, Alhaji Yunus Olalekan Saliu ya ce an fitar da zakkan ne domin rage talauci da inganta rayuwan wadanda suka amfana da shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Saliu ya yi kira ga masu hannu da shuni su rika tallafawa kungiyoyin zakka "domin rage radadin talauci da wahalhalu da kimanin 'yan Najeriya miliyan 80 ke fama da ita."

"Ina son in tunatar da cewa masu arziki ba za su iya morar arzikinsu ba idan ba su kulawa da talakawa da masu bukata," a cewarsa.

Shugaban kungiyar ta LEMU, Dakta Kamoru Omotsoho ya bukaci wadanda suka amfana da zakkan suyi amfani da abinda suka samu ta hanyoyin da suka dace domin fitar da kansu daga kangin talauci.

A wani labarin daban, Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya amince da nadin sabbin mataimakansa na musamman na bangaren dandalin sada zumunta 30 hakan ya kawo adadin hadiman da gwamnan ke da su zuwa 672.

A baya, Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya nada hadimai 642 da suka hada da manyan hadimai na musamman da jami'an tuntuba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel