Haramta Biza ga masu magudi: Mu ke da hakkin zaban wadanda zasu shiga kasarmu - Ingila ta yiwa Najeriya raddi

Haramta Biza ga masu magudi: Mu ke da hakkin zaban wadanda zasu shiga kasarmu - Ingila ta yiwa Najeriya raddi

- Jakadiyar kasar Birtaniya ta mayarwa najeriya martani mai zafi

- Birtaniya ta lashi takobin haramtawa duk wanda aka kama da magudi a zaben Edo shiga kasarta

- Hakan bai yiwa gwamnatin Najeriya dadi ba kuma ya mayar da martani

Gwamnatin kasar Birtaniyya ta ce duk da cewa tana girmama yancin kan Najeriya, ita ke da hakkin zaban wanda take so ya shiga kasarta ko ta bawa biza.

Jakadiyar Birtaniya dake Najeriya, Catriona Laing, ta bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron wayar da kai ga mutane masu nakasa dake neman minhan Chevening a UK.

Za ku tuna cewa Birtaniya ta yi barazanar haramta biza ga duk wanda aka kama da hannu cikin magudi ko rikicin zabe a Najeriya.

Amma hakan bai yiwa gwamnatin tarayya dadi ba inda ta ce wannan rainin hankali da cin mutuncin yancin kan Najeriya ne.

KU KARANTA: Ba zamu fasa zuwa yajin aiki - Kungiyar kwadago ta bayyanawa gwamnatin tarayya

Haramta Biza ga masu magudi: Mu ke da hakkin zaban wadanda zasu shiga kasarmu - Ingila ta yiwa Najeriya raddi
Credit: Presidency
Source: UGC

DUBA NAN: Jihar Gombe da Adamawa sun sanar da ranar bude makarantu

A cewar NAN, Catriona Laing ta ce Birtaniya ta amince da maganar cewa gwamnatin Najeriya na bibiyan wadanda sukayi magudin zabe, kuma ya jinjinawa zaben 19 ga Satumba da akayi a jihar Edo.

Ta yi bayanin cewa lamarin hana biza ga masu haddasa rikicin zabe tsari ne na gwamnatin Birtaniya.

"Wannan ka'idarmu ne na bada biza, mu ke da hakkin amincewa mutum shiga Birtaniya. Saboda haka, wannan ba lamarin yancin kai bane," Tace.
"Kuma dukkan abubuwan da muke fadi daidai ne da ka'idojin Najeriya, cewa duk wanda yayi rikici ko ya haddasa rikici zai iya fuskantan matsala idan ya nemi bizan shiga Birtaniya."

Yayinda take tsokaci kan shin Birtaniya za ta karaya kan martanin da gwamnatin Najeriya tayi; Laing ta ce gaskiya abin ya bata mamaki.

Ta ce gabanin zaben 2019, gwamnatin tarayya ta amince da wannan shiri, amma yanzu tana suka.

A baya, Gwamnatin tarayya ta bayyana bacin ranta kan jawabin da gwamnatin kasar Amurka da Birtaniya suka saki kan zaben gwamnan jihar Edo da za'a gudanar gobe da na Ondo da za'a gudanar ranar 10 ga Oktoba.

Gwamnati ta nuna rashin amincewarta kan haramtawa wasu yan siyasa samun bizan shiga Amurka saboda zargin tafka magudi a zaben Kogi da Bayelsa da akayi a 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel