Ba zamu fasa zuwa yajin aiki ba - Kungiyar kwadago ta bayyanawa gwamnatin tarayya

Ba zamu fasa zuwa yajin aiki ba - Kungiyar kwadago ta bayyanawa gwamnatin tarayya

- Kimanin makonni uku bayan kara farashin man fetur da wutan lantarki, ma'aikatan Najeriya zasu tafi yajin aiki

- Kungiyar NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta janye karin da tayi ko ta fuskanci zanga-zanga

- An kwashe sa'o'i biyar ana tattaunawa tsakanin gwamnati da NLC ranar Laraba

Kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC, a ranar Alhamis, sun yi watsi da hukunicn kotun ma'aikata da ta haramta musu zuwa yajin aikin da za'a fara ranar Litinin.

NLC da TUC sun bayyana hakan ne bayan baran-baran a ganawar da akayi tsakaninsu da gwamnatin tarayya a daren Alhamis.

Sakamakon karin kudin farashin wutan lantarki da man fetur, gwamnati da kungiyoyin sun gana ranar Talata amma suka gaza cimma manufa saboda gwamnatin ta ki janye karin kudin farshin mai.

Sakamakon haka kungiyar NLC da ta TUC suka alanta cewa ma'aikata suyi yaji fari daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, 2020.

Amma wata kotun ma'aikata dake Abuja ranar Alhamis, ta bada umurnin haramtawa kungiyoyin zuwa yajin aikin.

Alkali mai shari'a, Ibrahim galadima, ya bada umurnin ne bayan wata kungiyar mai suna Peace and Unity Ambassadors Association ta shigar da kara ta bakin lauyansu, Sunusi Musa.

KU DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta dakatad da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi

Ba zamu fasa zuwa yajin aiki - Kungiyar kwadago ta bayyanawa gwamnatin tarayya
Hoto: @channelsTv
Source: Twitter

KU DUBA NAN: Haramta Biza ga masu magudi: Mu ke da hakkin zaban wadanda zasu shiga kasarmu - Ingila ta yiwa Najeriya raddi

Martani da hukuncin kotun, shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya yi watsi da labarin, inda yace har yanzu ba'a gabatar masa da hukuncin kotun ba kuma wadanda suka shigar da karan ba ma'aikatansa bane.

Yace, "Ta yaya hakan zai shafeni tunda ba'a bani takardar kotu ba? Shin an bani ne? Ma'aikatanmu ne? Wani alaka nike da shi da wata kungiya?"

An karkare zaman gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago babu matsaya

Ganawar da aka fara misalin karfe 4:16 na rana a fadar shugaban kasa, ranar Alhamis kuma aka kammala misalin karfe 9:22 na dare babu maslaha.

Amma yayin jawabi ga manema labarai bayan zaman, ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyana cewa an dage zaman zuwa ranar Litinin domin kammala tattaunawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel